Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Bayan Wani Lokaci Fitacciya Jaruma Maryam Jankunne Ta Dawo Masana'antar Kannywood

 Bayan Wani Lokaci Fitacciya Jaruma Maryam Jankunne Ta Dawo Masana'antar Kannywood A yanzu haka dai tsohuwar jaruma a Masana’antar shiry...

 Bayan Wani Lokaci Fitacciya Jaruma Maryam Jankunne Ta Dawo Masana'antar Kannywood

A yanzu haka dai tsohuwar jaruma a Masana’antar shirya Fina finan hausa Kanywood Maryam Jankunne ta dawo harkar fim bayan ta shafe tsawon shekaru da ba a ganin fuskarta a cikin Masana’antar.Maryam ta shiga harkar fim a shekarar 2005 daga bisani tayi Aure a shekarar 2008. Jankunne na daya da ga cikin jarumai mata da suka taka rawa a masana’antar Kannywood a shekarun baya kafin tayi Aure.

Maryam tayi zamani da irin su Fati Muhammad, Rukayya Dawayya, Rashida mai sa’a, Mansurah Isah da sauran jaruman da suka yi fice a wancan lokacin.

Jarumar ta yi fina finai irinsu Jankunne kusan fim dinta na farko da ya fara fito da shi ne kuma ta samu lakabin Maryam Jankunne a cikin shirin.

A yanzu haka ana tsakar daukar sabon wani shirin da Maryam fito a cikinsa mai Suna AKASI shirin mai dogon zango, ya dauki jarumai kamar haka Abba El Mustapha, Saratu Gidado wato Daso da sauran jarumai.

Follow Us On Jakadiyararewa.com.ng for More New Updates

No comments