A Cewar Aisha Tsamiya Ba Gobe Ne Daurin Aure Na Ba Sai Nan Gaba Kadan BAYA ta haihu. Fitacciyar jaruma A’isha Aliyu (Tsamiya) ta bayyana c...
A Cewar Aisha Tsamiya Ba Gobe Ne Daurin Aure Na Ba Sai Nan Gaba Kadan
BAYA ta haihu. Fitacciyar jaruma A’isha Aliyu (Tsamiya) ta bayyana cewa ba a gobe Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 ba ne za a É—aura mata aure kamar yadda aka yaÉ—a a soshiyal midiya.
Wannan sabuwar sanarwar ta biyo bayan yaÉ—a wani katin gayyatar aure ne wanda aka yaÉ—a a soshiyal midiya, ana cewa na auren jarumar ne.
A katin, an nuna cewa fitacciyar jarumar za ta yi aure a ranar Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022.
A katin, wanda mujallar Fim ta gani, an bayyana sunan sahibin nata, wato Alhaji Buba Abubakar, kuma aka ce za a É—aura auren da misalin Æ™arfe 1:00 na rana a masallacin Sheikh Zarban da ke Kwanar ‘Yanwanki, kusa da gidan Tanko Yakasai da ke unguwar ‘Yankaba, a Kano.
Tun da labarin auren ya É“ulla a soshiyal midiya abokan sana’ar A’isha su ka shiga yi mata fatan alheri, inda kusan dukkan su sun É—ora hoton ta tare da katin auren.
No comments