Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Besty The Movie 2022 Kannywood Series Movie

  Besty The Movie 2022 Kannywood Series Movie Sai dai kasancewar ana yi ne domin 'yan kallo shine ma yasa furodusan fim din wato Bashir ...

 

Besty The Movie 2022 Kannywood Series Movie

Sai dai kasancewar ana yi ne domin 'yan kallo shine ma yasa furodusan fim din wato Bashir Maishadda (@realmaishadda) yake son jin ta bakin masoya akan irin salon da suke so fim din ya kasance, imma mai dogon zango ko kuma gudarin fim da za'a iya nunawa a Cinema rana daya.

Shidai wannan fim mai suna #BESTYTHEMOVIE fim ne wanda babban matashin mai daukar nauyin (producer) fina finan nan wato Bashir Maishadda zai fara daukar sa akan tsarin dogon zango nan bada dadewa ba, kuma fim din zai dauki hankali kasancewar duk masu kallon fina finan Hausa na masana'antar Kannywood suna sane da irin gagarumar rawar da matashin furodusa Bashir Maishadda yake takawa ta hanyar fitar da manyan fina finan Hausa na Cinema yau kuma gashi yace za fara fitar da mai dogon zango.

Shirin fim din Besty dai za'a tsara shi ne akan rayuwar wasu jaruman Kannywood da Isah A. Isa da Teema Makamashi da kuma shararriyar mai tallace tallace da sauran rikice rikice ta kafafen sada zumunta (social media) wato Sadiya Haruna ta take yiwa kanta lakabi da Sayyada Sadiya. Akan fadan da ya faru a tsakanin su duk a kan Besty wanda saida takai su ga shariar da a karshe ta antaya Sadiya Haruna gidan gyaran Hali (Gidan Yari). Allãh Shi kyauta. Dama dai ance kowa ya kwana lafiya shi yaso kuma tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka.

Shirin fim din Besty zai sami babbar kulawa ne daga:

Shiryawa

@realbasheermaishadda

Bada Umamarni

@adamzangoofficial

Muna nan muna dakon wannan kayataccen fim mai suna #BESTYTHEMOVIE
Zamu ci gaba da kawo muku rahotanni a dukkan gabar da wannan fim ya kasance in Allãh Ya yarda.

Besty The Movie 2022 Kannywood Series Movie

                                          ALKALAMI YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS


No comments