Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

DA ƊUMI-DUMINSA | Tsohon gwamnan jihar Kano Sen. Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP tare da magoya bayansa a wajen wani taron

 DA ƊUMI-DUMINSA | Tsohon gwamnan jihar Kano Sen. Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP tare da magoya bayan...

 DA ƊUMI-DUMINSA | Tsohon gwamnan jihar Kano Sen. Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP tare da magoya bayansa a wajen wani taron masu ruwa da tsaki na kafa wata sabuwar ƙungiya ta masu kishin ƙasa da suka shirya mai suna (The National Movement) wanda ya ƙunshi manyan jiga-jigan ƴan siyasa da ƴan kasuwa da ƙungiyoyin fararen hula.

Daga cikin jiga-jigan ƴan siyasar dake tafiyar sun haɗa da:

- Tsohon gwamnan jihar Kano HE Rabiu Kwankwaso, Kano 

- Tsohon gwamnan jihar Kogi H.E Captain Idris Wada.

- Tsohon gwamnan jihar Edo H.E Lucky Ignedion.

- Tsohon gwamnan jihar Kebbi H.E Adamu Alero.

- Tsohon gwamnan jihar Jigawa H.E Saminu Turaki.

- Tsohon gwamnan jihar Cross-river H.E Donald Duke.

- Tsohon gwamnan jihar Cross-river H.E Liyal Imoke.

- Tsohon gwamnan jihar ƙwara H.E Abdulfatah Ahmed.

- Tsohon gwamnan jihar Bayelsa H.E Serika Dicson.

-Tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa Prof. Attahiru jega.

-Tsohon shugaban hukumar bada tallafi ga jami'oin Najeriya Dr. Abba Bichi.

-Tsohon ministan matasa da wasanni Barr. Solomong  Dalung.

-Prof. Pat Utomi

-Buba Galadima

-Sen. Rufai Hanga

A yanzu haka ana cikin tsaka da gudanar da taron a Babban ɗakin taro na "National Conference Center" da ke babban birnin tarayya Abuja.

Karin bayani zai zo daga baya.

DAGA Comr Nura Siniya.

No comments