Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Duk Lokacin Da Na Ji Waƙar Mijina Marigayi Ahmad S. Nuhu Sai Hankalina Ya Tashi, Cewar Tsohuwar Jarumar Hafsat Sheh

  Duk Lokacin Da Na Ji Waƙar Mijina Marigayi Ahmad S. Nuhu Sai Hankalina Ya Tashi, Cewar Tsohuwar Jarumar Hafsat Shehu Tsohuwar matar fitacc...

 Duk Lokacin Da Na Ji Waƙar Mijina Marigayi Ahmad S. Nuhu Sai Hankalina Ya Tashi, Cewar Tsohuwar Jarumar Hafsat Shehu

Tsohuwar matar fitaccen tauraron Kannywood, marigayi Ahmad S. Nuhu, ta baiyana mawuyacin halin da ta tsinci kan ta  bayan rasuwarsa.

Hafsat Shehu ta bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa, a yayin da tauraron yake cika shekara 15 da rasuwa.

Jarumin ya rasu ne ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2007, sakamakon hatsarin mota a garin Azare na Jihar Bauchi.

Ta ce bayan rasuwar sa, ta faɗa cikin matukar bakin ciki yadda “idan na ga wasu mutane suna dariya nakan tambayi mahaifiyata cewa yaushe zan yi dariya’? Sai mama tace ki yi hakuri ke ma wata rana za ki yi.

Ta ce duk Lokacin da ta ji wani ya cewa Wata yana son ta sai hankali ta ya tashi Saboda itace kalma ta karshe da Mijina Ahmad S. Nuhu ya fadamin kafin ya tafi maiduguri wacce kuma ita ce tafiya da bai sake dawowa ba.

” Ahmad mutumin kirki ne Mai mutunta mace da kokarin Ganin ya faranta Mata ta hanyar sauke duk wani nauyi da Allah ya dora masa, inda ta ce "a  gaskiya na yi rashin masoyi kuma a lokacin da nake da buƙatar sa.”

Hasfat Shehu, bayan ta fashe da kuka ta ce "Alhamulillah Allah ne ya bani Ahmad Kuma ya karbi kayansa,Amma dai Ina so ku Sani wallahi ko Wakar sa aka sa ana daga min hankali.


"Amma dai Ina yi masa addu’a a ko da yaushe don nema masa rahamar Ubangiji," in ji ta.

No comments