Hukumar Karota Ta Rufe Duk Wata Tashar Mota Da Ke Hanyar Kurna, Rijiyar Lemo, Da Bachirawa. Daga Zaharaddeen Gandu Hukumar Karota da ke ji...
Hukumar Karota Ta Rufe Duk Wata Tashar Mota Da Ke Hanyar Kurna, Rijiyar Lemo, Da Bachirawa.
Daga Zaharaddeen Gandu
Hukumar Karota da ke jihar Kano, ta rufe duk wata tashar mota da ke kan hanyar Kurna, Rijiyar Lemo da Bachirawa, daga cikin manyan tashohin da aka rufe sun haÉ—a da: KTST, Aminchi, da kuma Kano Line.
Hakan ya faru ne tin safiyar ranar lahadin nan da misalin ƙarfe 9:00 na safe., Daga ƙarshe an baza jami'an Hukumar Karota domin su yi gadin tashoshin.
A yayin haɗa wannan rahoton, nayi ƙoƙarin jin ta bakin wani ma'aikacin tashar KTST inda ya bayyana min cewa:
"Ni kaina ban san da wannan dokar ba, saida nazo nan da mota sannan na sani, domin naga wani abokin aikina yana É—agamin hannu, alamun intsaya". Inji shi
Saide nayi ƙoƙarin jin daga bakin jami'an tsaron, saide bansamu damar jin ta bakinsu ba.
No comments