Idan Kwankwaso Ya Yafewa Ganduje, Wallahi Yan Kwankwasiyya Ba Zasu Yafewa Kwankwaso Ba – DanBilki Comamder Rikicin siyasar kano sai kara ...
Idan Kwankwaso Ya Yafewa Ganduje, Wallahi Yan Kwankwasiyya Ba Zasu Yafewa Kwankwaso Ba – DanBilki Comamder
Rikicin siyasar kano sai kara ruruwa takeyi inda ankaji jiya ne mai girma gwamnan kano Dr. abdullahi umar Ganduje ke cewa sabuwa kano kwankwaso ce da ganduje a wajen wani taro.
To shine ake rade raden ficewar kwankwaso daga jam’iyarsa pdp zuwa apc shine dan gwagwarmaya dan bilki kwamanda yayi magana akan zai iya yafewa Ganduje ga abinda majiyarmu ta samu daga gidan rediyon Nasara Radio Fm.
Danbilki Kwamanda yace idan har Kwankwaso ya yafewa Ganduje, to mutanen Kwankwaso (Yan Kwankwasiyya) ba zasu yafewa Kwankwaso ba, saboda babu wanda gana musu azabar siyasa sama da Ganduje, domin wasu har ransu suka sadaukar saboda kare darajar Kwankwaso.
Kwamanda ya bayyana haka ne jiya cikin shirin mu na “Inda Ba Kasa” a Nasara Radio (Amanar Talaka).
Ya kuka kalli wannan batu nasa?”
No comments