IZZAR SO EPISODE 78 YA DAUKI ZAFI Yayin da Izzar So ya dauki zafi yayinda al'amura suka hadu suka yamutse a cikin Kampanin Shinkafa na ...
IZZAR SO EPISODE 78 YA DAUKI ZAFI
Yayin da Izzar So ya dauki zafi yayinda al'amura suka hadu suka yamutse a cikin Kampanin Shinkafa na Maigirma Matawalle aka yi juyin juya hali sakamakon rikici tsakanin karya da gaskiya, wato bangaren su Hajiya Nafisa (Aisha Najamu) da kuma bangaren Umar Hashim (Lawal Ahmad) da tawagarsa.
A shirin da ya gabata na Izzar so kashi na 77 masu kallo sunga irin kulla-kullar da su Hajiya Nafisa da 'yan barandarta irin su Jibrin suka yi ta kai ruwa rana sai sun zartar da abin da zuciyar su take so, yayin da suka manta da cewa wannan masarrafa fa amana ce aka wakilta su akai amma suka dage domin ganin sun azurta kansu.
Idan bazaku manta ba a baya Hajiya Nafisa ta nemi ta bude hannun jari domin wani sashe na kamfanin ya zama nata sakamakon wani rade-radin cewar dan Matawalle wato Aliyu yana raye bai mutu ba, inda ta nemi canja jadawalin dokar Maaikatar domin ta zama mallakin ta dungurungum ta hanyar tursasawa masu rike da ofishi sai sun saka hannu domin canji.
Umar Hashim shine shine wanda yaki sa musu hannu amma kaidin Hajiya Nafisa bai barshi ba shine suka kullawa Karima sharri da Nakowa, ta yadda dole ya saka musu hannu ko kuma su fallasa ta kowa ya san halin da take ciki.
Yayin su Hajiya Nafisa suka kira taro domin fallasa da muzantawa ne, sai Maigirna Matawalle ya bayyana inda gaba dayan shirin su ya lalace har takai Maigirna Matawalle yasan halin da ake ciki a Maaikatar wanda ada bai sani ba. Hakan ya bakanta masa zuciya ainun ainun inda ya canjawa Maikatar fasali ta hanyar yi mata garen bawul yayin da ya sauke Hajiya Nafisa daga matsayin ta ya maye gurbin ta da Umar Hashim sannan kuma ya mayar da Karima manaja ya kuma bukaci Hajara Diyar Matawalle cewa ta kawo takardunta idan tana son aiki a Kamfanin, sannan ya kora Hajiya Nafisa gida domin HORO.
IZZAR SO 78