Kotu A Jihar Jigawa Ta Daure Wani Daurin Rai Da Rai Bayan Ta Same Shi Da Laifin Fyade Ga Yarinya Karama Babbar kotun jiha dake zaman ta a ...
Kotu A Jihar Jigawa Ta Daure Wani Daurin Rai Da Rai Bayan Ta Same Shi Da Laifin Fyade Ga Yarinya Karama
Babbar kotun jiha dake zaman ta a garin Birnin Kudu karkashin Mai Shari’a Musa Ubale ta zartar da hukuncin daurin rai da rai akan wani Mai suna Haladu Sani dake kauyen Mai-Rama dake karkashin Dagacin Bigidan na karamar hukumar Birnin Kudu bisa samunsa da laifin yiwa yarinya yar shekara 11 fyade.
Da yake zartar da hukunci Mai Shari’a Musa Ubale ya ce kotun bayan ta saurari shedu bakwai ta samu wanda ake karara da aikata laifin, inda ta zartar masa da hukuncin daurin rai-da rai karkashin sashi na 282 na kundin laifuffuka da hukunce-hukuncensu na Penal Code.
A halin da ake ciki kuma kotun ta sallami wani Usman Lamido Isah Baba na garin Adiyani dake yankin Karamar hukumar Guri bisa zargin aikata laifin kisan kai karkashin sashi na 222 hudu cikin baka na kundun penal code.
Haka zalika kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Musa Ubale ta sallami Sama’ila Sani na kauyen Tilli-Bukwui dake karamar hukumar Buji bisa zargin aikata laifin cin zarafi da aikata fyade karkashin sashi na 397 da 389 da kuma 282.
No comments