Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Kotu Tatisa Keyar Sadiya Haruna Zuwa Gidan Gyaran Hali Wato Prison

  Kotu Tatisa Keyar Sadiya Haruna Zuwa Gidan Gyaran Hali Wato Prison Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin daurin wata shida ba zabin tara a ka...

 Kotu Tatisa Keyar Sadiya Haruna Zuwa Gidan Gyaran Hali Wato Prison

Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin daurin wata shida ba zabin tara a kan tsohuwar ‘yar fim din Hausa na Kannywood, Sadiya Haruna kuma fitacciyar mai sayar da kayn mata, Sadiya Haruna a bisa laifin batanci ga wani darekta a harkar fina-finan, Isa I.Isa.

Kotun ta majistare wadda ke zama a filin jirgin sama na mallam Aminu Kano, ta same ta da laifin batanci ga darektan Isa I.Isa. wanda ya kai ta kara, a shafinta na Istagram, a yau Litinin 07 ga watan Fabrairun 2022.

Kotun ta kuma zartar da cewa kada wadda aka samu da laifin ta kara wani rabutu ko sanya wani abu a wani shafinta na sada zumunta da muhawara, wanda zai zama na batanci ga wani nan da shekara daya, idan ba haka ba za a sake yanke mata wani hukuncin na shekara biyu.

Sai dai kuma Sadiya Haruna tana da damar daukaka kara kan hukuncin kotun.

                         

No comments