Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

LABARI, An Yiwa Ango Musayen Mata A Cikin Zauren Daura Aure A Kaduna

  LABARI, An Yiwa Ango Musayen Mata A Cikin Zauren Daura Aure A Kaduna    Daga Muhammad Inuwa Zariya  Wani abun ban mamaki da ya faru a hayi...

 LABARI, An Yiwa Ango Musayen Mata A Cikin Zauren Daura Aure A Kaduna   

Daga Muhammad Inuwa Zariya 

Wani abun ban mamaki da ya faru a hayin rigasa dake cikin garin kaduna shine, an daurama ango aure Amma bada wacce suka yi soyayya ba a tun tale tale.

Alokacin da wakilin jaridan Alfijir Hausa ya tuntubi waliyin amaryan, ya shaida masa cewa uban waccen da sukayi soyayya mahaifin yarinyar bayason angon Sam hakanma da  kyar aka samu har aka kawo ga wannan rana na shirin daura auren yar nasa amma daga baya abun ya canza.

Kazalika Daya daga cikin mahalarta wannan zauren na wurin daura auren, Shi kuma dabi'un angon da tarbiyan sa ya yi mashi, shiyasa ya juya da auran kan 'yarshi na cikinshi nan take.

Uban da ya yi kaka gida a domin ganin aure ya dauru da yar shi, ba zato ba tsammani, daman ya yi kira ga kannensa cewa duk Wanda ya aurar masa da yaransa kotu ce za ta raba shi da koma waye, matsayar ba shi ne ya kawo masu mazajen aure ba.

 Bisani da aka zo daura aure ya shiga gida yaroki 'ya'yanshi ga duk wacce angon ya zaba zai daura mata auren dashi, daman mahaifin na su ya Riga da ya sayan ma yaran nashi komai ta kayan daki.

Bugu da kari Sukuma 'ya'yan nashi suka amince da bukatar da mahaifinsu ya zo masu da shi.

Wakilin na mu bayan ya waiwayi angon domin jiyo ta bakinshi, ya shaida mashi cewa, dama uban waccan budurwan nashi baya son ganinsu a tare daman yaiyin sane suka tilasta sai an daura masu aure, shi kuma yana gudun fishin iyayen waccan budurwan na shi ya lala masu aure sai yasa ya amince da wannan canji da aka samu ta matarsa.

LABARI, An Yiwa Ango Musayen Mata A Cikin Zauren Daura Aure A Kaduna


Wanan lamari ya farune a rigasa dake cikin garin kaduna a layin goburawa.

No comments