NARABU DA MIJINA SABODA KISHIN DA NIKE MA UWAR GIDA _*Mai tambaya:-*_ meya kaiki haka yar'uwa😲😲? Na yanke wannan hukuncin ne saboda sh...
NARABU DA MIJINA SABODA KISHIN DA NIKE MA UWAR GIDA
_*Mai tambaya:-*_ meya kaiki haka yar'uwa😲😲?
Na yanke wannan hukuncin ne saboda shine daidai
Kanaji na?
Tunda yake zuwa wajena ban tabajin ya kushe Uwar gidansa ba
Tun daga nan nasa kokonto a raina
Amman dayake Allah yayi dole sai na aureshi nayi 1year a dafe😫
Shin Uwar gidan nasa kuna fada ne da ita ko asiri takeyi.?
Subhanallahi AA bata ko daya hasalima yar uwa ta daukeni ko qanwa
Tana kama girman ta sosai
Mai tambaya; 'to ya akayi?'
Ranar dana shiga gidan tun a ranar ta fara samun yabo daga yan'uwa na saboda karramawa data musu
Mijina baizo da abokai ba dakina sai da Uwar gidansa da hannun sa tana riqe da ledar amarci
Suka zauna ta gaidani na amsa taimin ban gajiya
Sai naji tanacewa ango nizan wuce bacci ina maka fata Nagari, Allah kuma ya zaunar damu cikin aminci
Ya amsa da Amin sweetheart.
Ya sake rakata
Tun daga ranar a zatona makircine. Ashe tsantsan tsoron Allah ne da iya zama,
Da kyautatawa.
Tace har muka gama amarci ita ke mana komai...
Tace ranar da zai fita office ina daga daki nace mishi sai ka dawo ya fice abunsa.
Amman ranar girkinta sai naji yace zan fita sweetheart, Amarya zan fita
Sai naga wani sabon salo😄
Ta tsuguna ta sanya masa takalmi.....tace; wallahi ka dauka yaune aurensa ko tana da matsayi wajen fassion na maza❤
Ta dauko wani turare sai da ya gauraya dukkan girman falon nan sabida kamshi
Ta sanya masa agogonsa,
Rike da jakar sa har wajen mota ina ta leqensu😳
Sai naga ta bude masa, mota ina zaton zata dawo ciki
Sai naga ta shige motar😫
Maita fada masa? Sai Allah, sai naga ya zagayo ya dagota yana sumbatar kumatun ta...cikin farin ciki har yabar, harabar gidan tana daga masa hannu🤚🏻
Tace;
tsabar baqin ciki na shige daki ina sake saken ta ina zan fara; ni ga girman kai yai mini yawa
Ba abunda aka koyar dani banda shan maganin mata da aka koya min tamkar yar mai ganye😆😆😆
Tace; ina kwance yar'hutu
Tun wannan wankan safen da na yi har lokacin dawowarsa yayi.
Tace, fita falo da zanyi wani qamshi ya dokeni har sai da na rufe ido ina shigo falo ba kowa sai jerin abinci tamkar gidan biki🤣😆
Sai naji tsayuwar motarsa sai ji naji yaran ta suna Abba oyoyo sai ga uwar biye dasu cikin shiga ta debe hankali da qamshi
Duk suka yi waje
Yaran suka tafi da gudu suka rungume Abban su;
Suna dariya yeeeeeh mun riga mommy😄
Sai naga wani abun mamaki tamkar yarinya ta tsaya ta rike kafada adole tana shagwaba sun rigata!
Tsabar baqin ciki bansan sanda nace wawuya kawai🤣🤣
Bansan ashe nice wawuyar ba, wani salon shaquwa ne❤😍
Tace; sai naga ya sauke yarinyar hannunsa, yaje ya rungume ta, yana ce mata; 'sorry!' tare da yaran; 'Sorry mommy!' cikin barkwanci "irin na masoya
Yaseemin Tace; Mommy ai kin rigamu rannan, sai suka yi dariya duka suka dauko jaka domin rakiyar abansu zuwa falo nan take haushi yatikeni kamar namutu😫
Su ka yo cikin gida.
Nai maza na koma na zauna sai gashi yace; A'A
My luv 'babu welcome? Ashe kina falo? Sai na yi kici kici......you're welcome😕
Ya amsa; thank you!
Suka shige, yaran kuma sukai dakinsu tunda ba Islamiyya ranar,
Haka rayuwa ke tafiya tamkar ni ce Uwar gidansa😆😆😆.
Haka suke wankin kayan kicin oga (underwears) ya watsa mata kumfa ta rama suyi ta tsere a gida kamar yara.
Nikuma kullum alabe a window tamkar tsaka😆
Ci gaba;
Mai tambaya yai tattaki zuwaga mijin;
Yallabai ko maiyasa amaryar ka ta kasa zama da uwargida?
Shin ya Uwargida take gare ka?
Yace ita wani bangare ne daga cikin jikina
Nakan rasa duk farin ciki idan nayi nisa da ita
In takaita maka 'yar Aljanna ce,
Mai addini ce,
Mai kyauta ce,
Mai tsoron Allah ce;
Ta maida gidana tamkar filin Farin ciki,
Bata fushi dani.
Tana gode mini akan komai
Takan damu da damuwata
Tana haquri da farin cikinta saboda nawa
Takanyi wasa dani
Bata hangen wani gida akan nata
Bata shigar banza in zamu unguwa
Kwalliyar ta ni kadai takewa
Inada laifi idan nasota da yawa?
Mai tambaya A'A
To kanada wannan matar wa ya aike ka karin aure tunda ba ta gaza maka ba?
Qarin aure bai nufin gazawa,
Hasali ma yana cikin Sunna ta Manzon Allah
Daga cikin qaddara kuma.
🚶🏻♀🚶🏻♀Tattaki zuwa ga uwargida❤
Ranki ya dade menene sirrin ki na rike gidan ki?
❤ Hakuri da taimakon Allah ko yaushe da tarbiyar iyayena.
Tace;
Duk sanda mijina ya 6atamin idan ina tsaye nakan zauna na fitar da numfashi tare da cewa A'uzubillahi Minash Shaidanir Rajim.
Daga nan saina tuna bautar Allah nakeyi.
Sai na tuna cewa Manzon Allah SAW yace jarumi shine Wanda ya Iya mallakar kansa lokacin fushi.
Tace; ban taba sujjada ba tare da na nemi taimakon Allah cikin aure na ba.
Tace; nakan roki Allah sabunta son da mijina ya ke mini........
Sallar Dare
Sallar Walaha
Karatun Qur'an
Ta kuma dukkan nasara ana samunta a
Sadaka
Kyautatawa iyaye.
Allah ya sa mu dace
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________
No comments