Wata Amarya Ta Kashe Mijinta, Yayin Da Yazo Saduwar Aure Da Ita. Wata amarya yar shekara 18 ta kashe mijin ta har lahira, saboda ya kusance...
Wata Amarya Ta Kashe Mijinta, Yayin Da Yazo Saduwar Aure Da Ita.
Wata amarya yar shekara 18 ta kashe mijin ta har lahira, saboda ya kusanceta da niyyar yin saduwar aure da ita. Inda wannan mummunan al’amari ya faru a jihar Bauchi Najeriya, kamar yadda W-Tv ta rawaito.
Amaryar mai suna Salma wadda auren nasu bai kai sati biyu da daurawa ba, da bakin ta ta amsa wannan laifi da ake tuhumar ta da shi na kashe mijinta, wanda aka haÉ—a su auren zumunci tare.
Haƙiƙa wannan lamari akwai abin duba a cikin sa, sai dai ba lallai a fahimci asalin maganar ba, tunda shi dai mijin nata ya riga ya mutu balle aji ta bakinsa kamar yanda akaji daga bakinta.
Sai dai ita wannan amarya ta faɗa cewa ta daɓa masa wuƙa a kirjinsa ne, a lokacin da yazo gurinta zai raya sunna da ita, wanda kafin aje asibiti yace ga garin ku nan.
Yanzu haka zaku iya buɗe bidiyon da ke ƙasa, domin jin cikakken bayanin daga bakin wannan amarya yayin da 'yan jaridu ke fira da ita a cikin bidiyo: