Ba Mai Ajiye Kudi Sama Da Miliyan 5 A Banki Har Sai EFCC Ta San Da Su __Cewar Majalisar Dattawan Najeriya Daga Tukur Sani Kwasara Majalis...
Ba Mai Ajiye Kudi Sama Da Miliyan 5 A Banki Har Sai EFCC Ta San Da Su
__Cewar Majalisar Dattawan Najeriya
Daga Tukur Sani Kwasara
Majalisar dattawan Najeriya ta zartar da wani kudiri na yin gyara ga dokar kudaden ta shekarar 2011 da ke neman tilasta wa bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi su gabatar da rahoto a rubuce ga sashin da ke kula da hada-hadar kudade a karkashin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC
Kudirin dokar ya yi nuni da cewa duk wata harkallar kudade ga mutum daya tilo da ta haura naira Miliyan 5 ko kuma Kamfani da ta haura naira N10m to sai an sanar da Hukumar EFCC a rubuce.
Sashi na 11(3) na kudirin dokar ya tanadi cewa “duk wata cibiyar hada-hadar kudi da ta saba wa tanadin wannan sashe to ta aikata laifi kuma za a yanke mata hukuncin tarar kudi mai yawa, kamar yadda dokar ta tanada.
No comments