BUHARI NE YA CIRE MAI MALA BUNI --El-Rufai A Nijeriya Shugaba Muhammadu Buhari ya marawa kudirin tsige gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe da...
BUHARI NE YA CIRE MAI MALA BUNI
--El-Rufai
A Nijeriya Shugaba Muhammadu Buhari ya marawa kudirin tsige gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe daga kan mukamin sa na shugaban riko a jam'iyyar APC. Wannan bayani ya fito ne daga bakin gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai a wata hira da manema labarai suka yi da shi a tashar talbijin ta Channels ranar Talata.
El-Rufai ya ci gaba da cewa gwamnan jihar Neja Sani Bello ya sami cikakken goyon baya daga Shugaba Buhari da kuma ilahirin gwamnonin APC su goma sha tara 19 da ma wasu jigajigan jam'iyyar ta APC.
Ya kara da cewa dama tunda farko na fada muku cewa Shugaba Buhari shine ya cire Mai Mala Buni sakamakon wata almundahana da aka gano cewa gwamnan jihar ta Yobe yayi.
Bayan Buhari ya bada umarnin cire Mai Mala Buni sai ya mika sunan gwamna Sani Bello Isma'il na jihar Neija inda aka tabbatar da nadin nasa tare da goyan bayan gwamnonin APC 19 da wasu masu fada aji na jam'iyyar. Inji El-Rufai.
El-Rufai ya kara da cewa, duk fa wannan abun ya faru ne alhali Mai Mala Buni baya kasar, don haka idan ya tashi dawowa zai dawo ne a matsayin gwamna kawai ba shugaban jam'iyya ba.
Ku biyo mu don jin wasu sababbin labarai.
No comments