Cikakken Rahoton Matar Da Ta Kashe Mijinta Ta Hanyar Burma Masa Wuka A Wuya Sunan ta Atika 'yar asalinta wani kauye mai suna Kawari da...
Cikakken Rahoton Matar Da Ta Kashe Mijinta Ta Hanyar Burma Masa Wuka A Wuya
Sunan ta Atika 'yar asalinta wani kauye mai suna Kawari dake karamar hukumar Zango ta Jihar Katsina. Amma suna zaune da mijinta a garin Mararabar Abuja da jihar Nasarawa. Haihuwarsu hudu da mijinta amma 'daya ya rasu daga cikin 'ya 'yan su saura uku yanzu. Mijinta wanda ta kashe bakaniken mota ne sunan sa Ibrahim Ahmad.
Kusan watanni biyar da suka wuce ya kara aure, bayan ya yi sabon gidan da suka koma kusan shekara guda da ya gabata.
Atika ta kasance mai tsananin kishi suna yawan yin fada da mijinta, an yi mata shedar masifa sosai, kuma kafin Ibrahim ta fara yin wani aure, an ruwaito cewa shi ma tsohon mijinta na farko barazanar kai farmaki take yawan yi masa da wuka hakan ya sa ya rabu da ita, a baya ta taba yankan matar yayan mijinta da wuka a lokacin da suke fada suna gida daya kafin mijinta ya yi sabon gida su koma.
Ranar Asabar din da ta gabata da misalin karfe 08:00pm Ibrahim ya dawo gida kai tsaye ya wuce 'dakinta domin kai mata Golden Milk shigarsa ke da wuya sai rikici ya barke tsakaninsu, lamarin da ya kai su ga har ta gantsa masa cizo a hannu ta fasa hannun sa ta kuma yanka masa cizo a kirjinsaz shine ya fito da sauri ya nufi wajen dayan matarsa ya ce da ita ta daure masa hannunsa, bayan an daure masa hannun ya juya baya yana tafiya ita kuma ta sake fitowa ta zaro wuka ta biyo shi ta baya ba tare da ya sani ba ta burma masa a wuya (tsakanin kafadarsa da wuyansa) ta sake caka masa a gefen kirjinsa (kusa da hammatarsa) a lokacin ne Ibrahim yace da ita kin kasheni, kamar yadda take shedawa da kanta.
A lokacin ne kishiyar ta tayi sauri ta shige dakinta ta rufo kofa ta kulle kuma ba ta fito ba sai da ta tabbatar mutane sun shigo gidan.
Ibrahim ya fara gudu zuwa bakin kofar gida yana ihun neman taimako amma Atika ta sake zaro wata katuwar gora ta bi shi da gudu ta buga masa a kansa ta sake buga masa har sai da kwakwalwarsa ta fito ya kama kofar gidan (gate) hannunsa duk jini ga wuyan sa yana feshin jini, daga nan ya fadi ita kuma ta fara ihu tana cewa "na shiga uku na kashe mijina da hannuna".
An dauki Ibrahim zuwa asibiti, inda kafin a kai shi asibiti ya rasu.
Yanzu haka dai an yiwa Ibrahim jana'iza kamar yadda addinin islama ya tanadar, ita kuma tana hannun rundunar 'yan sanda ana cigaba da bincike.
Ya Allah Ka tsare mu da sharrin mata marasa imani ka bamu mata masu imani ka hana mu mu'amulla da su ta kusa da ta nesa.
Daga M Inuwa M.H
Rariya
No comments