Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Dalilin Karancin Wutar Lantarki

  Dalilin Karancin Wutar Lantarki Ministan Lantarki Injiniya Abubakar Aliyu ya bayyana cewa akwai dalilai da sune suka jawo rashin samun w...

 

Dalilin Karancin Wutar Lantarki

Ministan Lantarki Injiniya Abubakar Aliyu ya bayyana cewa akwai dalilai da sune suka jawo rashin samun wutar lantarki, duk da an shawo kan lamarin yanzu, amma dalilan sune karewar adadin makamashin kasa da matsalar lallata bututun mai da karancin iskar gaz da kuma matsalar dake tsakanin kamfanonin gaz da na wutar lantarki.

Ya bayyana hakan ne jim kadan da kammala zaman majalisar zartaswa da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar Shugaban Kasa yau Laraba.

kedco,Dalilin Karancin Wutar Lantarki

Aliyu ya bayyana cewa megawats 8,000 ne adadin makamashin da ake iya samarwa, idan aka samu rauni akai, dole a samu matsalar wutar lantarki a fadin kasar nan, amma ya bayyana cewa ana gab da kawo karshen lamarin. X

No comments