Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Martanin Da Jaruma Rukayya Dawayya Ta Maida Martani Daga Gidan Haya Kafin Ta Gina Nata

Martanin Da Jaruma Rukayya Dawayya Ta Maida Martani Daga Gidan Haya Kafin Ta Gina Nata  Rukayya Umar santa wacce aka fi sani da Rukayya Dawa...

Martanin Da Jaruma Rukayya Dawayya Ta Maida Martani Daga Gidan Haya Kafin Ta Gina Nata

 Rukayya Umar santa wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya Jarumar Kannywood wadda ta shafe kusan shekaru ashirin a masana'antar.

Ta fara fitowa a shekarar 2003 a wani fim mai suna Dawayya tare da Musbahu M ahmad, baya ga jaruma Rukayya kuma shahararriyar yar kasuwa ce.

Kamar yadda wasun ku kuka sani Rukayya Dawayya ta dauki tsawon lokaci tana gina gidanta inda za ta yi sauran rayuwarta.

Gidan da aka gina ya dauki hankulan jama'a saboda an yi shirin kashe makudan kudade.

Rukayya ta wallafa wani vedio a shafinta na Instagram inda ta bayyana cewa kafin ta gina nata gidan sai da ta zauna a gidan haya aka wulakanta ta aka kore ta, shi ya sa ta yi kokarin gina nata gidan domin guje wa irin wannan matsala. zuwa gaba.

Ta kuma kara da cewa ta samu matsala da danginta a lokacin da take son shiga harkar fim daga karshe danginta suka kore ta daga gidan.



Shi ya sa ita da kawarta suka nemi gidan haya da za su zauna, bayan wasu shekaru sai ta yi kasuwanci kuma ta samu nasara inda a yanzu ta gina nata gidan.

No comments