Tsadar Fetur: za a dakatar da gidajen mai masu kara farashi ~ Karamin Ministan Mai Daga Tukur Sani Kwasara Karamin Ministan Albarkatun Man ...
Tsadar Fetur: za a dakatar da gidajen mai masu kara farashi ~ Karamin Ministan Mai
Daga Tukur Sani Kwasara
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva, ya ce duk gidajen mai da ke siyar da man fetur da sauran kayayyakin mai da suka haura farashin da aka amince da shi, za a kakaba masu takunkumi.
Ministan wanda ya yi wa manema labarai karin haske a Abuja, ya ce: “Muna sane da cewa akwai wasu masu gidajen man da ke cin gajiyar rashin man fetur ta hanyar kara farashin kayayyakin man.
Ina tabbatar muku cewa za a sanya takunkumi ga duk wani gidan mai dake saida kayayyakin man ba kamar yadda aka amince ba.
Ministan ya bukaci ‘yan Nijeriya da su rika kai rahoton ‘yan kasuwa masu kara farashi ba bisa ka’ida ba, “Idan ba a bamu rahoto ba, ba za mu iya sanin abin da ke faruwa.”
Ya kuma ce tashin farashin danyen mai bayan rikicin Ukraine da Rasha na shafar farashin man fetur.
No comments