Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

According to Bobby Risky, the government should do the following before banning Gays.

  According to Bobby Risky, the government should do the following before banning Gays . Address Nigeria's Five Problems Before Applyi...

 

According to Bobby Risky, the government should do the following before banning Gays.

Address Nigeria's Five Problems Before Applying for a Penal Code

1, Addressing Insecurity Issues, 2, Resolving Power Outage Issues, 3, Addressing the Problem of Nigeria's Name Abroad

4, Put an end to the ASUU Akin Strike.

5, According to Bobrisky, market inflation should be reduced.


-Inji Bobrisky... namijin da aka sami nasarar mayar da shi mace.

Bob Risky wanda asalin sa namiji ne dan kabilar Yoruba wanda ya tashi da matukar nadamar kasancewar sa namiji, wanda a karshe likitoci suka sami nasararrar mayar da shi mace ta hanyar dashen kwayoyin halittar mace a dukkan sassan jikin sa dake nuni da alamomin mutum namiji ne.

Bobrisky dai dan asalin Nijeriya ne wanda a halin yanzu ya kasance mace domin kuwa ko a kafafen sada zumunta da suna mace yake amfani.

An dai haifi Bobrisky a shekarar 1992 a Ebute Metta, Ikeja Lagos a Nijeriya, kaga kenan a halin yanzu yana da shekara 30 a duniya.

Sunan Bobrisky na asali shine Okuneye Idris Olarenwaju ya kuma yi karatun sa na digiri a jami'ar Lagos, sannan ya fito a wani fim mai suna Ojuloge Obirin.

Biyo bayan kiran da majalisar tarayyar Nijeriya tayi akan saka dokar da zata bada dama a hukunta yan daudu Bobrisky ya kada baki ya kalubalanci gwamnatin Nijeriya akan haka. Inda yake cewa akwai fa matsaloli da yawa a gaban gwamnatin Nijeriya da ya kamata ta fara magancewa kafin tayi magana akan hana yan daudu rawar gaban hantsi kuma matsalolin ita gwamnatin duk ta sansu. Inda ya ce a halin yanzu yan Nijeriya ba wannan ne a gaban su ba face kawai su sami cikakken 'yancin watayawa a kasar su inda nan ne mahaifar su basu da inda ya fi ta. Yace ya kamata 'yan Nijeriya su sami aminci wajen tafiye tafiye a ko'ina a fadin Nijeriya (Right to movement).

Matsalolin da Bobrisky ya lissafa sun hada da:

 1. Magance matsalar tsaro.
2. Magance matsalar Rashin Wutar Lantarki.
3. Magance matsalar Kaurin Sunan da Nijeriya ta a Waje.
4. Kawo karshen yajin aikin ASUU.
5. Rage hauhawar farashin Kayan Masarufi da sauran su.

Bobrisky ya kara tabbatarwa da gwamnatin Nijeriya cewa akwai fa abubuwa masu mahimmanci da yawa wadanda a halin yanzu suka fi karfin 'yan Nijeriya su da kasar su ta haihuwa sakamakon babakere daga wasu tsirarun mutane.
YAKUBU ADAM ABUBAKAR (YACKSON)


Dandutse is a Jamilu shield.

No comments