Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Daddy Hikima Wanda Aka Fisani Da Abale Ya Ketare Iyakar Addini Da Kuma Na A'lada

  ABALE YA KETARE IYAKAR ADDINI DA KUMA AL'ADA A gaskiyar magana abubuwan da suke faruwa a masana'antar fim ta Kannywood sun sabaw...

 

ABALE YA KETARE IYAKAR ADDINI DA KUMA AL'ADA

A gaskiyar magana abubuwan da suke faruwa a masana'antar fim ta Kannywood sun sabawa tsarin zamantakewar Hausawa ta kowane sashe, domin kuwa gwadaben da aka dora fina finai a halin yanzu ya sauka daga kan layin addinin Musulunci da kuma al'ada wannan ne ma dalilin da yasa ake ta samun matsaloli ta ko'ina.

Duba da abin da Abale yayi a *gidan gala* ya kasance abin kaico da takaici a tsarin zananta kewar Hausawa domin a tsarin Hausawa babu maganar mace tazo ta rungumi namiji ko namiji ya rungumi mace amma sai gashi wannan ta'adar ta zama ruwan dare a wajen jaruman Kannywood wanda hakan bai dace ba kwata kwata.

*Adam Abdullahi Adam* wato *Abale* ko kuma kace *Daddy Hikima (Ojo)* wani babban jarumi ne wanda tauraron sa yake tashe a masana'antar fim ta Kannywood musamman ma tun lokacin da ya fito a wani fim mai suna *A Duniya.* Fim din *A Duniya* ya kasance daya daga cikin shahararrun fim masu dogon zango a masana'antar kannywood.

Abale dai jarumi ne da yafi fitowa a cikin wani salo irin na zafin rai da rashin tausayi a takaice da salon *Daba* da kurari  da kuma cin zali.

Anan ba akan iya *Abale* muke yin kira ba domin ba shi kadai ne yake yiwa Addini da Al'adu zagon kasa ba, wannan yana faruwa ne ga ilahirin jaruman masana'antar fim ta Kannywood.

Anan muna kara jan hankalin masu ruwa da tsaki akan tafiyar da sana'ar fim kamar Hukumar tace fina finai da kuma shugabannin masana'antar da su cire son zuciya tare da son abin duniya domin kawo gyara na ba sani ba sabo, ta yadda duk wanda ya saba daga dokokin da aka gindaya za'a ladabtar da shi ko wanene. Don haka yana da kyau a kiyaye domin irin su Abale na nan da yawa. Kuma Ba Yanzu Ake Jiba Gaba Akeji Tunda kowa Na San Ya Bar Baya Tunda Babu Wanda Zaiso Yaga Danshi Ko Yarshi Na Taba Jikin Wadda Ba Muharraminsa Ba Jamaa Don Allah AKula, Gyara  Muka Kawo Ayi Ba Wai Korafi Wani Ko Aybata Wani mukeso Muyi Ba Amma Gaskiya Ce Ita gaskiya Daci Ne Da Ita Don Allah Don Annabi A Gyara Wannan Abun Muna Godiya

Allãh Ka Tsaftace Mana Sanaar Mu

No comments