IZZAR SO EPISODE 82 ORIGINA HD Izzar so ya kara daukar zafi a sakamakon faruwar abubuwa masu rikitarwa duba da yadda lissafi ya kwacewa i...
IZZAR SO EPISODE 82 ORIGINA HD
Izzar so ya kara daukar zafi a sakamakon faruwar abubuwa masu rikitarwa duba da yadda lissafi ya kwacewa iyayen gayya.
Sai ku biyo mu a yau domin ganin yacce zata kaya tsakanin maigirma Matawalle, Hajiaya Sara da kuma Hajiya Nafisa wadda itace jigon wannan fim na izzar so shiri mai dogon zango wanda kuma shine na daya a manhajar youtube domin kuwa shine fim din kannywood mai dogon zango wanda aka kallon sa a duk mako.
Masu kallo sun yi cirko cirko suna jiran suga mene ne sakamakon wannan kara da hajiya Nafisa tayi yayin da Matawalle (Ali Nuhu) ya fada mata gaskiyar magana akan cewa ita ba diyar sa bace 'yar tsintuwa ce ita.
Wannan tonon silili ya faru ne duk a cikin alwashin da Hajia Sara tayi na ganin bayan Hajiya Nafisa duk da cewa Matawalle ya sa doka akan kada a fada mata cewa ba diyar sa bace don kar a sa mata damuwa, amma sai gashi saboda neman duniya Hajiya Sara ta fito a cikin wata sifa da ake kira komai ta fanjama fanjam bata ma damu da ko meye zai biyo baya ba.
A bangare daya kuma diyar Matawalle ta asali Hajara tana can a nata bangaren tana shirin neman aiki a ma'aikatar Mahaifin ta domin ta tarar da cakwakiya iya cakwakiya inda wasu daga cikin ma'aikatan suke neman durkusar da ma'aikatar ta hanyar azurta kansu. Saidai bata san ita kuma a tacan gefen Hajia Sarah ta sa an sace takardunta na karatu ba don haka idan aka bukaci ta kawo takardun baza ta gansu ba.
Ya dai kamata ku biyo mu domin ganin yadda zata kaya a yau da misalin karfe 9:00 na dare.
YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS).
No comments