Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Jerin Jaruman Kannywood Iyaye Mata Da Sukafi Iya Acting A shekara Ta 2022

  *WACE CE TAFI BIRGE DA KUMA KAYATAR DA KU A CIKIN WADANNAN KWARARRUN JARUMAN KANNYWOOD?* Zamu iya cewa duk mutumin da ya kwana ya tashi ...

 

*WACE CE TAFI BIRGE DA KUMA KAYATAR DA KU A CIKIN WADANNAN KWARARRUN JARUMAN KANNYWOOD?*

Zamu iya cewa duk mutumin da ya kwana ya tashi kuma ya kasance mai kallon fina finan Hausa musamman ma na masana'atar Kannywood dole yasan wadannan hazikan matan wadanda suke fitowa a matsayin iyaye kuma bazai manta da irin rawar gani da suke takawa a dukkannin fina finan da suka fito a cikin su ba.

Su dai wadannan mata sune kamar haka:

*1. Hajia Hajara Usman*

*2. Hajia Saratu Gidado (Daso)*

*3. Hajia Hadiza Muhammad (Hadizan Saima)*

Da yawa daga cikin masu kallo kowa yana da irin zabin sa akan kowane jarumi sakamakon kowa akwai irin aktin din wanda yake birge shi.

To amma dai yabon gwani ya zama dole koda baya birge ka idan gaskiya tazo dole ka fada. 

Hajara Usman, Saratu Gidado (Daso) da kuma Hadizan Saima jarumai ne guda uku da basu da na hudu indai ana maganar iya sarrafa shirin fim ne kai kace da gaske ne abin da suke gabatarwa, ga iya magana da azanci da sauran siddabarun fim ba  sigar da basu iya fitowa kuma su gabatar da ita lafiya.

To shine muke so muji daga bakin ku masu kallo yau dai muna so ku fayyace mana wacce tafi iya fim a tsakanin wadannan mashahuran jaruman da muka bayyana sunayen su a sama domin kuwa kune alkalai.XXXXX

Muna jiran raayoyin ku cikin sauri muga wacece mafi rinjayen kuria.

Hajara Usman dai kamar yadda kuka sani ta kasance uwa ga dukkan jaruman Kannywood mazan su da matan su ta fito a cikin daruruwan fina fina a matsayi uwa ko kuma kakar jaruman Kannywood. Hajara Usman takan fito a kowace irin siga, imma sigar salihai ko kuma mafadaciya kuma sai ka rantse haka ne asalin halinta.

Hajara Usman ta sami lambobin yabo da kyautuka da dama a masana'antar Kannywood sakamakon irin bajintar da take nunawa a cikin fina finan da ta fito a cikin su.

Itama Saratu Gidado Daso ba'a barta a baya ba kasancewar itama taga jiya taga yau ta kuma yi fina finai da shararrun jaruman Kannywood inda mafi yawancin sigar da tafi taka rawa a kanta itace sigar rashin mutunci da makirci da fada da rigima duk da cewa ba halinta bane a zahiri amma fa ta kware sosai waje kacaccala jarumi ko jaruma musamman in ya zama su suna da kudi ku kuma kuka fito a talakawa to a nan ne zaku ga tijara.

Ta ukun su kuwa ita ce Hadizan Saima wadda tazo daga bayan su amma fa saida ta kusan kawo karshen kowacce jaruma musamman wadda take fitowa a matsayin uwa badon komai ba tazo ne da mabambancin salon da yasa ko wane darakta da furodusa suke son yin aiki da ita domin yana bayar da irin abin da ake so har ma a kari.

Jerin Jaruman Kannywood

Hadizan Saima kyakykyawa ce dadin dadawa domin kuwa duk da cewa tana da shekaru amma sai kaji mutum yana cewa shi ko a haka zai iya auren ta. Gaskiya dai tazo da sigogi da yawa da za ta iya shafe duk wata jaruma da take fitowa a matsayin uwa.


No comments