Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Saratu Gidado Daso Ta Hadu Da Wani Gagarumin Wani Abun Alajabi A Wajan Raba Abinci

 SARATU GIDADO (DASO) TA TALLAFAWA MARAYU DA ABINCI A WATAN AZUMI Shararriyar yar wasan kwaikwayon nan ta Nijeriya a masana'antar sh...

 SARATU GIDADO (DASO) TA TALLAFAWA MARAYU DA ABINCI A WATAN AZUMI

Shararriyar yar wasan kwaikwayon nan ta Nijeriya a masana'antar shirya fina finai ta Kannywood, Saratu Gidado da ake fi sani da Daso tace ita ma bazâ a barta a baya ba wajen kwasar falalar dake cikin watan azumin Ramalana inda aka hangi sananniyar jarumar a wani gidan marayu inda ta kawo musu abinci mai yawa da kuma dan karen dadi. Inda ta rarraba mu musu domin rage musu wani radadin.Irin dai dai wannan al'adar ta taimakekeniya ita ce irin al'adar da ake so dukkan Musulmi suyi koyi da ita domin kuwa hali ne mai kyau kuma koyarwa ce ta Fiyayyen Halitta Sallallahu Alaihi Wasallam.

Anan muna kira ga daukacin al'ummar Musulmi da su tashi tsaye sannan a zage dantse wajen tallafawa marasa galihu ta kowacce fuska mutum yake da dama.

Abin ba haka yake ba mutum yace wai sai masu tarin dukiya ne suka cancanci su yi taimako. Ko kusa abin ba haka yake ba kai dai kawai ka tsarkake niyya wajen bayar da abin da ya sawwaka komi kankantar sa Allah Ya san manufar ka cewa da kana da mai yawan ma to zaka yi taimakon ne da yawa.







Saratu Gidado Daso tayi namijin kokari kuma muna fatan za'a yi koyi da ita cikin shaanin ciyarwa saboda falalar sa. 

A karshe muna yiwa jarumar fatan alheri akan sadaukarwa.

YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS)

No comments