KING KHALIFA YAYI WASA (PERFORMANCE) TARE DA JUNAIDIYYA GIDAN BADAMASI King Khalifa Ya kayatar da yan kallo a wani wasa da yayi a gidan ...
KING KHALIFA YAYI WASA (PERFORMANCE) TARE DA JUNAIDIYYA GIDAN BADAMASI
King Khalifa Ya kayatar da yan kallo a wani wasa da yayi a gidan wasa tare da kyakykyawar jarumar fim mai suna *Junaidiyya Gidan Badamasi* inda suka yi amfani da wata sabuwar wakar sa mai suna *Ke Nake So* wakar da dai waka ce ta soyayya mai ratsa zuciya tare da nishadantarwa. Ya kuma fitar da bidiyon wakar a salo mai jan hankali da annushuwa.
*King Khalifa* matashin mawaki ne wanda ya jijjiga duniyar waka inda wannan sabon album da ya fitar ya zama irin sa na farko a *Arewacin Nijeriya* kuma tabbas ya kara kima ga mawakan na Arewa.
King Khalifa ya karbi babbar kyauta (award) irin sa na farko da aka taba samu a *Arewacin Nijeriya*. Babu shakka dole a jinjinawa wannan matashin mawakin *King Khalifa* saboda irin rawar da ya taka a wakokin sa cikin su har da wata waka mai taken *Suna Na*.
Mawakin yayi matukar basira ta fuskar amfani da wannan kyakykyawar kuma kwararriyar matashiyar jarumar *Gidan Badamasi* domin kuwa sun dace sosai da wakar kai kace dama su masoya ne tun fil'azal.
Muna taya King Khalifa murnar samun wannan daukaka da kuma kayatacciyar kyauta.
*YAKUBU ADAM ABUBAKAR (YACKSON)*
No comments