Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Safarau Ta Dauko Ruwan Dafa Kanta Tunda Gwamnatin Kaduna Na Nemanta

  Safarau Ta Dauko Ruwan Dafa Kanta INA TAUSAYIN MACEN DA DUK TA ZABI IRIN WANNAN RAYIWA.  Wannan rayiwa da wannan yarinya ta daukar ma ka...

 

Safarau Ta Dauko Ruwan Dafa Kanta

INA TAUSAYIN MACEN DA DUK TA ZABI IRIN WANNAN RAYIWA. 

Wannan rayiwa da wannan yarinya ta daukar ma kanta wallahi bamai bullewa bace, kawai wasu ne za suyi anfani da ita su samu kudi, dazaran shekarun ta sunja kuma anfanin ta ya kare.

Yanzu wani Namiji ne zaiyi sha'awar auren wannan yarinya, ko wani Namiji koda shi Dan iska ne, burin sa shine ya auri mace ta kirki ba mutumiyar banza irin sa ba, wannan yarinya abin kunyar Da ta yiwa kan ta da iyayen ta bazai taba goguwa ba har abada.

Kamar bata da iyaye? Kamar iyayen ta basu damu da rayiwan ta ba? Kamar ba Amana Allah ya basu ba? Kamar basu san wannan abin da take yi bai dace ba? Kamar basu san mutuncin yarsu yafi komai muhimmanci  a rayiwa ba? Kodai sun tsinceta ne akan hanya? Ai koda tsintar da suka yi basu san iyayen ta ba, bai dace su zaba mata irin wannan rayiwa ba.

Cikin matasan da suka taru suna kallon ta tana rawa har suna bata ashirin-ashirin inda kanwar su ce, ko mahaifiyar su take irin wannan rawa ba zasu tsaya kallo ba, amma dake yar wasu ce iyayenta suka kasa bata tarbiya babu ruwan su.

Safarau

Wato Irin wannan rayiwa karshen ake tinani ba farkon ba, karshen yafi farkon muni. 

Allah ya shirye ta, yasa ta gane Amin.

Daga Ismail Bawa.

No comments