Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Sako Na Musamman Ga Masu Ibadar Umrah

Sako Na Musamman Ga Masu Ibadar Umrah Daga Mahmud Isa Yola Kwanan nan malamai suka yi ta gargadi akan masu yada hotunan Umrah da aikin h...

Sako Na Musamman Ga Masu Ibadar Umrah

Daga Mahmud Isa Yola

Kwanan nan malamai suka yi ta gargadi akan masu yada hotunan Umrah da aikin hajji a yayin da suke gabatar da ibada a social media, wanda yin hakan na iya saka mutum yayi asarar ibadar sa gaba dayan ta saboda riya.

Amma kamar an watsawa wuta fetur, kawai sai ga sabon salo. Yanzu addu'a da ake yi wanda mutum yana yin sa ne tsakanin sa da Allah SWT, sai kaga ya saka ana masa bidiyo a yayin da yake yin addu'ar, sannan kuma idan ya gama, sai yazo social media ya saka bidyon. Wannan wani irin tunani ne?

Shin kana rokon Allah ne ko kana rokon 'yan Social Media? Allah kam a social media yake ne da sai ka dauko abunda ka roka kana sakawa a social media? Anya akwai tsarkake niyya a nan?

Wannan abun takaici ne matuka saboda idan ka duba mai yin hakan ya dau hanya ne na riya. Ita kuma riya tana lalata aikin ibada kamar ba a yi ba. Saboda haka masu ibada su mayar da hankali a nan, su kuji dukkan abunda zai lalata musu Ibada. Muna muku fatan alkhairi.

No comments