2023 Alhaji Atiku Abubakar Ya Lashes Zaben Fidda Gwani Na Wannan Zaben 2023 Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya...
2023 Alhaji Atiku Abubakar Ya Lashes Zaben Fidda Gwani Na Wannan Zaben 2023
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023. Atiku Abubakar ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa da aka gudanar ranar Asabar a Abuja, babban birnin kasar.
Ya samu kuri’u 371 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas wanda ya samu kuri’u 237. Sai kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, wanda ya samu kuri’u 70.
Cikakken bayanin kuri’un da ‘yan takarar suka samu sune kamar haka. Atiku Abubakar
Alhaji Atiku Abubakar da Sauran Gwamnoni
Atiku Abubakar – 371
Nyesom Wike- 237
Bukola Saraki – 70
Udom Emmanuel – 38
Bala Mohammed - 20
Pius Anyim – 14
Sam Ohabunwa – 1
Olivia Tariela - 1
Akwai kuri'u 12 marasa rinjaye
Mai zuwa…
