Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Jaruman Kannywood Mata 5 Wadanda Ba 'Yan Najeriya Ba

 Jaruman Kannywood Mata 5 Wadanda Ba 'Yan Najeriya Ba Duk masana’antar fim da ta yi kaurin suna a duniya, takan tara jarumai kala-kala ...

 Jaruman Kannywood Mata 5 Wadanda Ba 'Yan Najeriya Ba

Duk masana’antar fim da ta yi kaurin suna a duniya, takan tara jarumai kala-kala da kabilanci daga kasashe daban-daban na duniya.To wannan shi ne abin da ya faru a masana’antar kannywood kasancewar ta daya daga cikin manyan kamfanonin fina-finai a Afirka inda ta tara manyan jarumai daga kasashe daban-daban musamman na Afirka.

A yau mun kawo muku kadan daga cikin jaruman kannywood wadanda ba yan Najeriya ba.


1. HADIZA ALIYU GABON

Adizatou Aliyu, wacce aka fi sani da Hadiza Gabon, fitacciyar jaruma ce a masana’antar fina-finan kannywood a Arewacin Najeriya.

An haifi Hadiza Aliyu  Gabon a Libreville, babban birnin kasar Gabon a ranar 1 ga watan Yuni, 1989. Hadiza Gabon ta fito a fina-finai da dama irin su Indon Kauye, da Gidan Badamasi na Arewa24.


2. IZZATU ZEENAT

Kyakyawar jaruma Izzatu peenat na daya daga cikin jaruman kannywood da ba 'yan Najeriya ba.

An haifi Izzatu ranar 11 ga Oktoba, 2000 a Jamhuriyar Nijar. Izzatu ta kasance daya daga cikin fitattun jarumai mata a kannywood da ta shigo da kafar dama.

Jaruma Izzatu Peenat ta fara fitowa a fim a shekarar 2018 kuma tana fitowa a wani fim mai suna Izzatu tare da taimakon fitaccen jarumin kannywood Ali Nuhu Sarki India ta baiwa jarumar damar gwada bajintar ta.


Ta fito a fina-finai da dama kamar Izzatu, Wutar Kara, So da So, Bala da Babiya, Sirrin Raina, Ciwon Ido, Komai Dare, Bakwai Bakwai da dai sauransu.




No comments