Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

JARUMAN KANNYWOOD ZA SU KARRAMA ALHAJI HAYATU MALIYA

 *JARUMAN KANNYWOOD ZA SU KARRAMA ALHAJI HAYATU MALIYA* Mun hango jaruman babbar masana'antar shirya fina finai ta Kannywood dake Nijeri...

 *JARUMAN KANNYWOOD ZA SU KARRAMA ALHAJI HAYATU MALIYA*


Mun hango jaruman babbar masana'antar shirya fina finai ta Kannywood dake Nijeriya zasu bada lambar girmamawa da karramawa ga wani dankasuwa dake kasuwar Kofar Wambai, na hannun dama kuma hadimi ga tafiyar Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano *Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna* mai suna *Alhaji Hayatu Maliya Gama Bridge* sakamakon jajircewar sa ga Gwamnatin jihar kano a karkashin tutar jam'iyyar *A.P.C.* musamman ma halaccin da yake nunawa tafiyar *Dr Nasir Yusuf Gawuna* ta kowane bangare. 

Alhaji Hayatu ya kasance jajirtacce wajen tallafawa al'umma musamman ma dai talakawa masu karamin karfi tanyar gina makarantu na Islamiyya da na karatun zamani kai harda tituna masu tarin yawa domin saukaka tafiye tafiye a unguwar Brigade da kewayenta.

*Alhaji Hayatu Maliya* bai tsaya nan ba domin ya kan dauki nauyin dalibai izuwa makarantu daban daban har sai sun kammala karatun su. Sannan *Maliya* yana bawa matasa jari domin suyi sana'oi daban daban na dogaro da kai, da kuma dakile zaman kashe wando da kuma bata gari.

A bangaren addini kuwa *Alh Hayatu Maliya* ya gina Masallatai da makarantun Islamiyyu a gurare daban daban a jihar Kano musamman ma a yankin Bridge.

Irin wadannan ayyuka na alheri da yake ta shimfidawa al'umma yasa Jaruman Masana'antar Kannywood suka ga ya cancanci a karrama shi domin kara masa kwarin gwuiwa da kuma zaburar da masu hali su yi koyi da shi wajen ayyukan alheri da yake wa jama'a.

*Alhaji Hayatu Maliya* jajirtaccen mutum kuma dan akidar *Dr Nasir Yusuf Gawuna*

Allãh Ya Kara Maka Kwarin Guiwar taimakawa al'umma.

*YAKUBU A. ABUBAKAR (YACKSON)*📖🖋️📝

No comments