Sumayya Says She Is In Love With Governor Ganduje Wata kyakykywar matashiya mai suna Sumayya dake unguwar Janbulon Kabuga a cikin birnin Kan...
Sumayya Says She Is In Love With Governor Ganduje
Wata kyakykywar matashiya mai suna Sumayya dake unguwar Janbulon Kabuga a cikin birnin Kano tace tun lokacin da ta taso a rayuwar ta bata taba ganin mutumin da take so a zuciyar ta irin gwamnan jihar Kano wato Abdullahi Umar Ganduje ba. Tace shine irin kalar mutumin da take son yi soyayya da shi a rayuwar ta domin kuwa ya mallaki duk wata irin siffa da take so taga namiji yana da ita don haka ne ma take fatan Allah Ya sa gwamnan yasan da ita ko zata yi sa'a shima yaji yana son ta.
Da ake yi mata tambaya cewar "bata ganin shi Ganduje ya manyanata ma'ana yayi mata tsufa atafau domin a ka'da ita jika ce ko kuma karamar 'ya a gare shi sai ta kada baki tace " ita fa soyayya ba haka take ba domin kuwa shi so ruwan sa da tsufan mutum al'amari ne na bugawar zuciya don haka ita dai a wajen ta Ganduje shi ne bugun zuciyar ta kuma tana son sa har cikin zuciya".
Da aka tambaye ta a game da matar sa Goggo wato Uwargidan gwamnan jihar ta Kano wato Hajiya Hafat Ganduje da kuma irin tasirin da take da shi a wajen Gwamnan, sai tayi farat tace "bata damu ba kuma ma bata wani damu ba da ko wacece matar sa domin shi namiji mijin mace hudu ne Ganduje na da dama ya kara auren wata koda bayan ya aure ta ne ma. Sannan ta kara da cewa " kowa fa da halin sa zai zauna ba da halin wani ba kuma shi zamantakewar aure al'amari ne na kowa tasa ta fishshe shi don haka ba wani sabon abu bane a rayuwar aure ki zamo kishiyar sa'ar babar ki ko kakarki ma". Ta kuma kara da cewa ita fa a shirye take domin tunkarar kowane irin kalubale domin kuwa ita ce tace taji ta gani.
Da farko mutane sun dauka cewar da wasa take yi ta yi wannan magana ne domin tayi suna wato itama a santa kamar yadda wasu yan mata suke tashe a kafafen sada zumunta da ake yayi a halin yanzu, amma a tattaunawar da wakilan mu suka yi da ita wannan matashiyar kyakykyawar yarinya wato Sumayya sai ta tabbatarwa da mutane cewa ita fa wannan lamari ba kirkirar sa ta yi ba kawai ta tsinci kanta ne tsundum a cikin soyayyar Ganduje kamar dai yadda kowane mutum yake tsintar kansa ba tare da yayi aune ba. Allah shi kyauta.
Masu iya magana sunce inda rakanka kasha kallo
ALKALAMI YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS)
To Get the Latest New Of Ganduje
CLICK THE LINK BELOW
CLICK HERE 1An Yi Kira Ga Tinubu Da Ya Ɗauki Ganduje A Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Zaɓen 2023
CLICK HERE 2 2023: 'Yan Arewa Tinubu za su zaba shugaban kasa - Ganduje
No comments