Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Jarumar Fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi Ce Ta Fi Shahara A Google A Shekarar 2021

Jarumar Fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi Ce Ta Fi Shahara A Google A Shekarar 2021 .Mazauna Abuja Ne Suka Fi Neman Bayanai Game Da N...

Jarumar Fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi Ce Ta Fi Shahara A Google A Shekarar 2021

.Mazauna Abuja Ne Suka Fi Neman Bayanai Game Da Nafisa Abdullahi

X

 Nafisa Abdullahi  Tana Da Mabiya Miliyan 2 A Shafinta Na Facebook

 Nafisa Abdullahi  tauraruwar fim É—in Labarina, ita kaÉ—ai ce 'yar Kannywood da ke cikin 10 na farko mafiya shahara a Google Search a 2021

 Nafisa Abdullahi Tauraruwar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi na cikin jerin taurarin da aka fi neman karin bayani a kansu a shafin matambayi-ba-ya-É“ata na Google Search a shekarar 2021 a Najeriya.

Tauraruwar Nafisa Abdullahi ta fim É—in Labarina ta shiga jerin ne tare da taurarin fim na kudancin Najeriya da ake kira Nollywood irin su Destiny Etiko da Tonto Dikeh da Zubby Michael.

Sai dai Google ya saka  Nafisa Abdullahi a É“angaren Nollywood maimakon Kannywood, wanda nan ne take ciki ya zuwa lokacin haÉ—a wannan rahoton.

Ita ce a matsayi na shida a sashen taurarin fina-finai bayan Destiny Etiko da Zubby Michael da Pere da Tonto Dikeh da Iyabo Ojo da kuma Olu Jacobs.

Jarumar Fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi Ce Ta Fi Shahara A Google A Shekarar 2021

Haka kuma,  Nafisa Abdullahi ce kaÉ—ai daga taurarin Kannywood da ta shiga cikin taurari 10 na farko a Google Search.

Sauran 'yan Kannywood Rahama Sadau da Fati Washa da Maryam Yahaya da Hadiza Gabon ne ke biye mata a shahara, duk da cewa ba sa cikin goman farko.

Shafin Google kan fitar da kalmomi da sunaye da ababen girki da mutane waÉ—anda miliyoyin masu amfani da shafin suka fi bincikawa duk shekara.

Sannan shafin kan yi wa sunayen rukuni, inda ake da rukunan mawaka da wakar kanta da wasanni da 'yan fim da fina-finan kansu da tambayoyin da aka fi yi.

 Nafisa Abdullahi na da mabiya miliyan biyu a Instagram da 176,600 a Twitter da kuma wasu miliyan biyu a Facebook.A É“angaren fina-finai, 'yan Najeriya sun fi neman bayanai kan Squid Game da Coming to America 2 da Sex Life da Black Widow da kuma Red Notice.

Daga cikin waɗanda suka rasu a 2021 kuwa, shahararren malamin Kirista TB Joshua da mawaƙi Sound Sultan da kuma Sani Dangote - ƙani ga Aliko Dangote - na cikin waɗanda aka fi dubawa.


Matakan Shaharar Nafisa Abdullahi

Kamar yadda bayanai suka nuna, Nafisa ta fara shahara ne a shafin daga ranar 3 zuwa 9 ga watan Janairun 2021.Hakan ba zai rasa nasaba ba da kammala kashi na 2 na fim ɗinta mai dogon zango wato Labarina, inda aka haska zangon ƙarshe a ƙarshen watan Disamban 2020.Masu neman bayanai kan tauraruwar sun ƙaru zuwa kashi 93 a watan Satumba, wanda a daidai lokacin ne ake tsaka da haska kashi na 3 na Labarina.

Bugu da ƙari, masu bincika Nafisa Abdullahi sun ƙaru zuwa kashi 100 cikin 100 daga 5 zuwa 11 na watan Disamba. Wannan kuma idan ba ku manta ba, yana da nasaba da kayayyakin ƙawa da ta ƙaddamar mai suna NAFCOSMETICS.

Mazauna Abuja babban birnin Najeriya ne suka fi neman bayanai game da Nafisa, sai kuma jihohin Rivers da Legas da Kaduna.

Sirrin Shaharar Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi ta kwana biyu ba a ganinta a harkar fina-finai kafin fara haska fim É—in Labarina a 2020.

Fim É—in wanda kamfanin Saira Movies na Aminu Saira ke shiryawa, ya samu Nafisa Abdullahi a matsayin babbar jaruma wadda aka gina labarin a kanta.

Tun bayan fara haska Labarina babu wani fim da  Nafisa Abdullahi ta fito a ciki wanda ya yi kusa da farin jinin

Ads h