Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

MATAN KANNYWOOD 3 DA SUKA DAWO FIM GADAN-GADAN

 MATAN KANNYWOOD 3 DA SUKA DAWO FIM GADAN-GADAN Kamar dai yadda kuka sani a masana'antar fina finai ta Kannywood dake Arewacin Nijeriya ...

 MATAN KANNYWOOD 3 DA SUKA DAWO FIM GADAN-GADAN

Kamar dai yadda kuka sani a masana'antar fina finai ta Kannywood dake Arewacin Nijeriya akwai shahararrun kuma sanannun mata da suka daina fitowa a cikin fina finai sakamakon aure da suka yi, to fa wasu daga cikin su sun dawo sakamakon yankewar da  igiyoyin auren su yayi, wasu kuma sun tafi wasu harkokin da bana fim ba.

A halin yanzu zamu yi muku albishir da dawowar wasu shahararrun mata guda 3 da suka dawo harkar fim gadan gadan.Da farko dai zamu fara gabatar muku da...

1. FATI MUHAMMAD

Fati Muhammad dai wata shararriyar jarumar fim ce a Nijeriya kuma 'yar siyasa. Tana kuma daya daga cikin jarumai mata da suka yi shuhura.Fati Muhammad ta koma harkar fim ne bilhaqqi, bayan ta shafe tsawon lokaci bata fitowa a fim.


A 2011, Fati Muhammad ta yi ta auri Umaru Kanu, wani furodusan fim wanda shi yaya ne ga Mawaki Ali Isha Jita wanda a yanzu basa tare.

2. AMINA UBA HASSAN

Amina Uba Hassan, wadda aka fi sani da Maman Haidar ita ma sanniyar jarumar fim ce a masana'antar fina finai ta Kannywood dake Nijeriya, ta kuma shiga masana'antar ne tun farko farkon 2000. Tsohuwar matar wani babban jarumi ce mai suna Adam Abdullahi Zango wadda kuma itace mahaifiyar dan sa na farko, Haidar Aliyu wanda ta haifa a 2008.Amina da Adamu sun rabu bayan wata biyar da haihuwar Haidar.

3. MARYAM MUHAMMAD

Ta ukun kuwa itace Maryam Muhammad ita ma tana daya daga cikin jarumai mata da suka hakaka a babbar masana'antar fina finai ta Kannywood dake Nijeriya.

Maryam Muhammad wadda tafi yin shuhura da suna Malika wanda a fim ta samo shi, ita kanwa ce ga marigayiya Balaraba Muhammad wadda ita ma jarumar fim ce kafin tayi aure.

Maryam Malika dai ta daina fitowa a fim sakamakon aure da ta yi. Amma a halin yanzu jarumar ta dawo harkar fim a 2020 bayan da suka rabu da mijin da ya aure ta saboda wasu dalilai.

YAKUBU A. ABUBAKAR (YACKSON)

Ads h