Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

WAKAR TA'AZIYYAR HADARIN RUWAN BAGWAI TA AMINU RINJI TA BAR BAYA DA KURA

  WAKAR TA'AZIYYAR HADARIN RUWAN BAGWAI TA AMINU RINJI TA BAR BAYA DA KURA Wakar Hadarin Ruwan Bagwai Wadda Shahararren mawakin nan mai ...

 WAKAR TA'AZIYYAR HADARIN RUWAN BAGWAI TA AMINU RINJI TA BAR BAYA DA KURA


Wakar Hadarin Ruwan Bagwai Wadda Shahararren mawakin nan mai suna Aminu Rinji Bagwai yayi a karo na biyu ta janyo cece kuce a tsakanin al'umma.

Mutane dai suna tofa albarkacin bakin sune kancewa a wannan karon mawakin ya saka siyasa a cikin sha'anin sa, suna cewa maimakon ya nunawa masu fada a ji kuskuren su sai ma mara musu baya da yake yi a cikin kalaman sa wanda suna ganin cewa ba daidai bane.

Idan baza ku manta ba a baya can da dadewa irin wannan hadarin ya taba faruwa wanda ya hada da shi kansa wannan mawakin. A sakamakon hakan ne mutane da yawa suka rasa rayukan su Allãh da ikon Sa ya tseratar da Aminu Rinji a cikin irin kalaman nan da Hausawa ke cewa: "Mai rabon ganin badi..." Ko kuma "wuya bata kisa*...

To fa wannan hadarin ruwan na farko shine asalin daukakar sa domin kuwa bayan ya tsira daga irin wannan tashin hankalin ne ya tafi studio domin ya fadawa duniya abin da ya faru a salon waka. Hakan sa kuwa ya cimma ruwa domin mutane sun karbi sakon sa cikin tausayawa har ya kasance dalilin da ya janyo masa daukaka.

To wannan ne ya sa mutane suke ta korafi akan marawa "yan siyasa baya da yayi a wakar tasa ta hadari ruwan karo na biyu inda suke cewa duba da yasan wahalar da ake sha a hadarin amma hakan bai sa ya fadawa mahukunta abin da ya dace ba duk kuwa da cewa yasan zafin da wadanda abin ya shafa suka ji...To ko me yasa Mawakin yayi amfani da wannan salon na yabawa jagororin siyasa a karo na biyu?

YAKUBU A. ABUBAKAR (YACKSON)

No comments