TARON ADDU'A TA MUSAMMAN GA WADANDA SUKA RASU A MASANA'ANTAR FINA-FINAN KANNYWOOD 'Yan masa'antar shirya finafinai ta Kanny...
TARON ADDU'A TA MUSAMMAN GA WADANDA SUKA RASU A MASANA'ANTAR FINA-FINAN KANNYWOOD
'Yan masa'antar shirya finafinai ta Kannywood sun gabatar da taro na musamman na addu'oi ga abokan ayyukansu da suka rasu.
Taron wanda Gidauniyar Kannywood, watau KANNYWOOD FOUNDATION ta shirya, an gudanar da shi ne a cibiyar matasa da ke unguwar Gyadi-gyadi a birnin Kano.
Taron ya samu halartar masu rike da mukami a gwamnati, da masu ruwa da tsaki na masana'antar, da masu fada a ji, da tsaffi da kuma sabbin jarumai na masana'anta mata da maza, da kuma sauran jama'ar gari.
Hotuna: Khalid Musa, Shehu S. Bello