Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Ana wata ga wata: Itama Kwankwasiyya ta samu Yan G7

 Ana wata ga wata: Itama Kwankwasiyya ta samu G7  Da alama dai tawagar yan bakwai sun bulla a Kwankwasiyya, domin wasu jiga-jigan siyasar gi...

 Ana wata ga wata: Itama Kwankwasiyya ta samu G7 

Da alama dai tawagar yan bakwai sun bulla a Kwankwasiyya, domin wasu jiga-jigan siyasar gidan tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a kalla mutane bakwai suka nuna alamar tirjiya a gare shi, har ta kai ga ana zargin cewa sun kauracewa Kwankwaso a wannan tsakanin, wanda bisa al'ada idan yana Kano, manya da yara a tafiyar na tare dashi, amma yanzu wadancan yan bakwai sun kaura. 

Wani mai suna Uba Magaji Galadima, ya taba bayyana wata tafiya mai suna "Restoration" a Kwankwasiyya, wacce ta kunshe mutane irinsu Yunusa Adamu Dangwani, Aliyu Sani Madaki, Aminu Dala, Zainab Audu Bako, Yusuf Bello Danbatta, Danburam Abubakar Nuhu da kuma Umar Kuliya, wanda yace akwai wasu abubuwa na rashin dai-dai da ake aiwatarwa a Kwankwasiyya, a matsayinsa na makusanci ga tsohon kwamishinan kasa da safayo, Yusuf Bello Danbatta. 




Jar Hula wata babbar alama ce a Kwankwasiyya, wacce ke alamta mutum a matsayin mai goyon bayan Kwankwaso, kuma a yanzu ita kanta jar hular tayi kaura a kawunan wasu mabiyan wadancan yan bakwai, wanda ko a watan da ya gabata, an jiyo Kwankwaso yayi wani shagube akan masu shirin tsallaka titi, abinda ya alamta cewa lallai akwai wata a kasa, kuma zamu cigaba da bibiya domin jin yadda zata kasance. 

Muna fatan dai Kwankwaso bazai kira su sunan "Banza Bakwai" ba, kamar yadda gwamna Ganduje ya ambaci nasa. 




No comments