Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Zalincin Yan Karota A Kano Idan Baa Tashi Tsaye A Kan Wannan Zalincin Ba To Wallahi Kasuwan cin Kano Da Tattalin Arzikin Kano Zai Karasa Mutuwa

Zalincin Yan Karota A Kano Idan Baa Tashi Tsaye A Kan Wannan Zalincin Ba To Wallahi Kasuwan cin Kano Da Tattalin Arzikin Kano Zai Karasa Mut...


Zalincin Yan Karota A Kano Idan Baa Tashi Tsaye A Kan Wannan Zalincin Ba To Wallahi Kasuwan cin Kano Da Tattalin Arzikin Kano Zai Karasa Mutuwa

Yau wani abu da na gani ya sani tunani matuka akan shugabanni a Kano; 'yan KAROTA na gani sun debo kayayyakin talakawa masu saye da sayarwa a tituna da sunan yin kasuwanci akan hanya ba bisa ka'ida ba. Abinda na gani an kwaso shine ya sani kusan zub da hawaye. Maimakon na ga shaddodi da atamfofi da takalma sai naga su goruba da mafitai da kwalba da nono da rake kai har da su gyada da dankalin Hausa. 

Abinda ya fara zuwa zuciya ta shine duk wadannan kayayyakin masu sayar da su sune cikakkun talakawa masu neman dan abinda zasu ci. Amma wasu shugabanni su kuma aikinsu akan wadannan talakawan yake karewa. Allah sarki saboda su basu da wanda zasu kai kukansu shine yasa idan an tafi da kayan nasu sai dai suyi Allah ya isa. Allah ya isan da wasu shugabanni suka dauketa ba komai ba. 

Karota



Da yawan talakawan da ake karya tattalin arzikinsu ta kwashe kayan sayarwarsu ta haka suke mutuwa saboda bakin ciki da ra ba su da dukiyoyinsu. Abinda na sani da kai mai karanta wannan dan rubutun nawa ka sani shine Rabbil Izzati baya barci kuma baya mantuwa sannan kuma komai ya yi masa lokaci. Sannan a karshe akwai ranar hisabi.

No comments