Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Ba Irinku Producers Da Directors Suke Nema Ba Daga Datti Assalafy

  NAZIRU SARKIN WAKA BAI KAMA SUNAN WATA BA DAGA Datti Assalafiy Ga wata wai ita jaruma a Masana'antar Hausa film mai suna Suwaiba Abuba...

 NAZIRU SARKIN WAKA BAI KAMA SUNAN WATA BA

DAGA Datti Assalafiy

Ga wata wai ita jaruma a Masana'antar Hausa film mai suna Suwaiba Abubakar tayi rantsuwa da Allah cewa babu wani Darakta ko furodusa da ya taba nemanta da lalata kafin ya sakata a shirin film. 

Tace wai ta shekara kusan 15 tana shiri film amma ba'a taba nemanta da lalata ba kamar yadda Naziru yayi zargin ana nemansu da lalata. 

Abin mamaki, shi dai Naziru Sarkin Waka bai kama sunan wata jaruma ba, me yasa Suwaiba ta tsargu? sannan ni ban taba sanin wannan matar da take kiran kanta wai ita jaruma ba a Kannywood. 

Ba ma raina halittar Allah, amma su kansu masu tarwatsa yaran mutane suna lalata da su ai ba irin wannan siffar suke nema ba. 

Ba Irinku Producers Da Directors Suke Nema Ba Daga Datti Assalafy


Allah Ka shiryar da su.

No comments