TSAKANIN DR ABDALLAH GADAN KAYA DA MATA LIKITOCI DAGA Datti Assalafiy Na karanta sakon wasu mata Likitoci suna kira ga Sheikh Dr Abdallah U...
TSAKANIN DR ABDALLAH GADAN KAYA DA MATA LIKITOCI
DAGA Datti Assalafiy
Na karanta sakon wasu mata Likitoci suna kira ga Sheikh Dr Abdallah Usman Gadon Kaya akan ya janye kalmomin da ya fada akan mata Likitoci da suke aikin Asibiti, imba haka ba zasu dauki mataki su kalubalanceshi
Menene Sheikh Dr Abdallah ya fadi akan Mata Likitoci da suke aiki a Asibiti har ya jawo suke neman daukar mataki ko raddi a gareshi?
Sheikh Dr Abdallah ya fara jawabi da cewa:
Wani Ma'aikacin lafiya ne ya taba jin wani wa'azina, sai yazo yake fadamin yace Malam Wallahi ni ma'aikacin lafiya ne, ina aiki a daya daga cikin manya l-manyan Asibitoci a jiha kaza, yace na san matar Aure ta kai shekara 50 da wani abu, ta dade tana aikin Likitanci amma Wallahi ba'a kyale ta ba, yace to yanzu wannan idan da mai shekara 40, 50 ba'a kyaleta ba, to ina ga yarinya karama da ta gama jami'ah tayi sabon aure take aiki a Asibiti?
Ance mata su je suyi karatun nan na Likitanci, su yaye mana bakinci, amma yace Wallahi Malam a ma'aikatun lafiyan nan kamar sauran ma'aikatu mutum ya bar matansa taje gurin aiki tana kwana bai dace ba sam, saboda tsarin aiki ne irin na YAHUDANCI, tsari ne ba na MUSULUNCI ba, sai a hada mace da na miji suyi aikin kwana a office guda, Nurses ne gaba dayansu, don haka tana aikin kwana wani Saurayi Balagagge shima yana aikin kwana
Zata je gurin aikin dare na kwana daga ita sai 'yar fangalalliyar riga, shikenan dole bacci ya kamata, dole kuma ta dan kishingida, shima namijin haka, kuma a daki daya, idan kayi wasa ma teburi ne guda, kujera ga wata kujera, su tura kofa su rufe, karfe uku na dare babu kowa, daga ita sai shi sai shaidan, meye ba za'ayi ba?
Kai magidanci kana can gida kana ta birgima sauro yana ta cizonka matarka Likita ta tafi aikin dare a Asibiti tana bacci da wani a daki guda
Yace Wallahi matan nan mai shekaru 50 sai ta dena zuwa aiki, aka tura mata takardan tuhuma (Query), tace eh a kawo zan amsa, aka kirata aka zauna da ita akace me yasa bakya zuwa aiki, tace eh, na ce ku barni nayi aikin rana amma anki, tace banyi zina ina yarinya 'yar shekara 14, 15, 16 ba, to ya za'ayi nazo yanzu ina zina ina da shekara 40 zuwa 50?
Aka tambayeta me ya faru Hajiya? tace nema na ake a aikin dare, waye yake nemanki? tace kowa ma, duk wanda muke aikin dare da shi, daga nan sai aka mata canjin gurin aiki aka mayar da ita wani Asibitin, sai taje ta tarar da aikin dai duk iri daya ne da Asibitin da ta baro
Sheikh Dr Abdallah yace ina yin wannan bayanin ne don Allah Ya isar da wannan sakon zuwa ga masu idanuwa da kunnuwa da masu tsoron Allah da zasu taimaki al'ummar Musulmi su tsare darajar matan mu a Asibitoci
Idan ba mu je makaranta munyi karatun ba kaskanci, idan mun tura matan namu sunyi karatu ba aminci, a kalla dai ya kamata ace mai raba aikin idan zai sa aikin dare ya hada mata guda biyu su kwana ba tare da na miji ba, kuma kar ka manta fa, su kansu matan da zasu kwana ba mamaki duk maza zasu duba a sashin da suke, to anji lalura ne, me zai hana ka hadata da 'yar uwarta mace mana, amma ba zasuyi ba
Kana magana cewa ya kamata a gyara, a ware bangaren mata dabam da na maza a Asibiti sai suce maka ai ba MUSULUNCI akeyi anan ba, a Kasarmu, a garin mu, a jihar mu, komi namu Musulmi, amma daidai da Asibitocin mu mun kasa controlling dinsu?, mu kwatanta mu kamanta tsari irin na Musulunci amma ya gagara
Akan samu daidaikun shugabannin Asibiti ko manyan Likitoci suna kula da mace Likita mai aure ko marar aure wajen saka ta aikin dare, wasu shugabannin Likitocin suna dan lura, amma wasu ba abinda ya damesu, ba mamaki ma shugaban Asibitin ba Musulmi bane, amma wannan zancen ku tambayi ma'aikatan Asibiti su fada muku, duk wanda yaki wannan zancen sai dai idan baya tsoron Allah
Wannan shine abinda Sheikh Dr Abdallah ya zayyana ba tare da ya kama sunan wata Likita ba, har ya jawo yanzu suna neman suci mutuncinsa
Bai kai sati guda ba, BBC Hausa sunyi hira da wasu Likitoci mata suke fadin kalubalen da suke fuskanta, har hakan ya jawo ba'a damuwa a auri mata Likitoci, mata Likitocin da kansu suka fadi haka a BBC
Gwamnonin jihohin Arewacin Nigeria Musulmai suna da karfin ikon da zasu kawo gyara a magance wannan barna da lalata, to amma da yake ba damuwarsu bane basa kulawa
Maganar da Dr Abdallah ya fada akan Likitoci mata gaskiya ne, muna tare dashi dari bisa dari, duk wanda taji haushi to halinta ne aka tona mata asiri, ku dauki duk matanki da kuke ganin zaku iya dauka
Muna fatan Allah Ya bamu shugabanni na kwarai da zasu Musuluntar da tsarin aikin Asibiti a Arewa
No comments