"Buhari Yafi Matasa Da Yawa Ƙoshin Lafiya". Cewar Garba Shehu . Daga Zaharaddeen Gandu Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba ...
"Buhari Yafi Matasa Da Yawa Ƙoshin Lafiya". Cewar Garba Shehu.
Daga Zaharaddeen Gandu
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa “Shugaba Buharin yafi mafi yawan matasan da suke ƙalubalantarsa a kan matsayin lafiyarsa, ƙoshin lafiya”.
Garba Shehu ya faɗi hakan a ranar Alhamis, yayin wata hira da yayi a Channel TV, a tsarin allon gani – gaka na (zoom).
Buhari, yanzu haka ma yana Brussels da Belgium domin halattar taron ƙoli na shida 6 na ƙungiyar haɗaka ta tarayyar Turai da Africa (EU-AU).
” shugaban ƙasa garau yake. Mu a gurinmu, abin burgewa shi ne, mutane sun fara jin daɗin cewa shugaban ƙasa yana cikin ƙoshin lafiya, kamar yadda wasu daga hotunan nan suka nuna”.
”Mun sha faɗa cewa, shugaban yafi da yawa daga cikin matasan da suke ƙalubalantar sa akan matsayin lafiyar sa, koshin lafiya. Hakan ko ya bayyana karara daga abin da ya fito daga ƙasar Belgium”. Inji Garba Shehu
Tunda ya kama aiki, shugaba Buharin yake jele zuwa kasar Birtaniya, akan matsayin lafiyar sa ; lamarin da ya janyo Sanya alamomin tambaya akan koshin lafiyar shugaban.
A wani rahoto da jaridar The Cable suka wallafa, a shekarar 2021, an gano cewa Buhari ya shafe kimanin kwanaki ɗari da saba’in 170 a ƙasar Birtaniya yana fafutukar lafiyarsa, tun bayan shigarsa Ofis.