DA DUMI DUMI Fati Slow Ta Karbi 1 Million Daga Nazairu Sarkin Waka Ta Hannun Mansura Isa Haka Allah Azurta Mutum Ta Inda Yakeso A Faruwa Wa...
DA DUMI DUMI Fati Slow Ta Karbi 1 Million Daga Nazairu Sarkin Waka Ta Hannun Mansura Isa
Haka Allah Azurta Mutum Ta Inda Yakeso A Faruwa Wannam Cece Kuce Da Ta Taso Tsohuwar JARUMA FATI SLOW Ta Sami Kyautar 1 Millon Yanzu Daga Naziri Sarkin Waka Bayan Tayi Wani Video A Shafinta Na Tik Tok Kamar Yadda Naziru Yayi Alkawari Tabba Wannan Cece Kuce Ya Jawa Fato Slow Alheri Allah Ya Bawa Masanaantar Kannywood Harukri Kuma Yakara Zaman Lafiya Ga Jatuman agaba Daya Mun Gode Daga Jakafiyar Arewa
Bayan Hakan Kuma An Samu Sulhu Gaba Daya Bashir Mai Shadda Da Sauran Mutanem Da Sukayi Kalamai A Batun Zancen An Samu Sasanci
MOPPAN ta sulhunta matan Kannywood da Naziru Ahmad a daran yau litinin 14/02/2022.
A DAREN yau Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta yi taron sulhu tsakanin Ƙungiyar Matan Kannywood (K-WAN) da fitaccen mawaƙin Kannywood kuma jarumi, Naziru M. Ahmad.
Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, shi ne ya kira taron a Kano don sulhunta ɓangarorin biyu a kan rikicin da ya ɓarke a tsakanin su.
Naziru Sarkin Waƙa ya yi iƙirarin cewa a Kannywood ba a sanya mace a fim sai ta bada kan ta.
K-WAN ta ba shi wa'adin kwana uku daga yau ya janye wannan kalamin nasa ko kuma ta maka shi a kotun shari'ar Musulunci a kan tuhumar ɓata suna.
MOPPAN ta yi sauri ta kira taron ne kafin lamarin ya ƙara ƙazancewa.
Shugabar K-WAN, Hauwa A. Bello, da shugaban Ƙungiyar Furodusoshi ta Arewa (AFMAN), Sani Sule Katsina, na daga cikin mahalarta taron.
Shi ma Naziru Sarkin Waƙa ya halarta.
No comments