Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Girgin Sama Na Air Peace Sunci Mutunci Sarki Aminu Ado Bayaro Da Tawagarsa

  Girgin Sama Na Air Peace Sunci Mutunci Sarki Aminu Ado Bayaro Da Tawagarsa Wani daga cikin ‘yanuwan Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu ...

 

Girgin Sama Na Air Peace Sunci Mutunci Sarki Aminu Ado Bayaro Da Tawagarsa

Wani daga cikin ‘yanuwan Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya rubuta takardar korafi zuwa ga hukumar NCAA ta tarayya. 

Daily Trust ta ce Isa Sanusi Bayero wanda aka fi sani da Isa Pilot ne ya aika wasika ga NCAA a kan abin da ya kira cin mutunci da aka yi wa Sarkin Kano. 

Isa Sanusi Bayero ya zargi kamfanin jirgin Air Peace da cin zarafin Sarki da mutanen kasar Kano. 

A wannan takarda ta korafi, Alhaji Isa Pilot ya koka a kan yadda jirgin saman ya bata masu lokaci daga Banjul zuwa Legas, inda suka bata sama da sa’a guda. 

Bayan haka, ‘danuwan Sarkin ya fadawa hukumar NCAA cewa kamfanin jirgin saman sun yi sanadiyyar da Mai martaba ya rasa jirgin da ya tashi zuwa Kano. 

Kamar yadda Platinum Post ta kawo rahoto, Sarki Aminu Ado Bayero da ‘yan tawagarsa sun iso tashar jirgin na Legas ne minti 30 bayan jirgin Kano ya tashi. 

Isa Pilot ya ce ya kira shugaban kamfanin Air Peace, Allen Onyeama, ya fada masa halin da ake ciki, ya nemi alfarmar a daga tashin jirgin da zai je Kano. 

An saba yi irin haka, a bata lokaci wajen tashin jirgin sama domin a girmama wani mai mukami ko martaba. Amma Allen Onyeama ya ce sam ba zai yi ba. 

“Nan take ya fada mani cewa ba zai yi wannan ba. 

Na dauki wannan a matsayin cin mutunci da kuma rashin daraja Mai martaba da duka mutanen Kano.” 

Isa Pilot Pilot ya ce dole Sarki da mutanensa suka kama otel su na jiran wani jirgin ya zo. A haka kuma sai da aka bukaci su biya karin kudi saboda sun ki hawa jirginsu. 

Girgin Sama Na Air Peace Sunci Mutunci Sarki Aminu Ado Bayaro Da Tawagarsa

Shugaban NCAA na kasa, Kyaftin Musa Nuhu ya samu wannan wasika, amma bai ce uffan ba.

No comments