Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

KAICO: Wani Matashi A Jihar Gombe, Ya Shake Mahaifiyarsa Ta Mutu Har Lahira, Saboda Ta Mishi Nasiha Akan Ya Daina Shaye-shaye

 KAICO: Wani Matashi A Jihar Gombe, Ya Shake Mahaifiyarsa Ta Mutu Har Lahira, Saboda Ta Mishi Nasiha Akan Ya Daina Shaye-shaye Daga Comr Abb...

 KAICO: Wani Matashi A Jihar Gombe, Ya Shake Mahaifiyarsa Ta Mutu Har Lahira, Saboda Ta Mishi Nasiha Akan Ya Daina Shaye-shaye

Daga Comr Abba Sani Pantami

A jiya Laraba, hukumar 'yan sanda reshen jihar Gombe ta jera wasu mutum takwas da ta kama da laifi daban-daban a faÉ—in jihar. 

Jaridar The Nation ta rahoto cewa É—aya daga cikinsu, Garba Abubakar, ya shiga hannu ne bisa zargin shakare mahaifiyarsa, Salamatu Abubakar, yar shekara 45.

Kwamishinan yan sandan jihar Gombe, Ishola Babaita, ya ce wanda ake zargin ya yi wa mahaifiyarsa haka ne saboda ta masa faÉ—a ya daina shan miyagun kwayoyi.

"Wanda ake zargi ya shake mahaifiyarsa ne saboda ta masa faÉ—a ya dena ta'amali da miyagun kwayoyi. An yi gaggawar kai matar babban Asibitin Kumo, amma likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa."

"Ina shawartar iyaye su maida hankali da sa ido wajen kula da 'ya'yan su kuma su tabbatar ba su faÉ—a muguwar É—abi'ar shan miyagun kwayoyi ba." 

Ya Kashe Mahaifiyar Sa


"Babban abun takaici wannan matar ta rasa rayuwarta a hannun É—an da ta tsugunna ta haifa, É—aya ne daga cikin sharrin kwayoyi."

No comments