Ina Tsoron kada a sace man Ɗa na shiyasa na cire shi daga Makantar Gwamnati______El-Rufa’i Rufa’i yace ya cire ɗanshi ne daga Makarantar G...
Ina Tsoron kada a sace man Ɗa na shiyasa na cire shi daga Makantar Gwamnati______El-Rufa’i
Rufa’i yace ya cire ɗanshi ne daga Makarantar Gwamnati, sabudda tsoron kada a sace shi.
A cewar sa, ya santa ɗanshi a Makarantar Gwamnati domin tabbatar da ƙudirin sa na yarda da tsarin ilmin Jahar Kaduna.
El-Rufa’i ya bayyana haka a ranar Alhamis a lokacin jawabin Kwamitin Shugaban Ƙasa akan Sadarwa a Villa, Abuja.
Ya bayyana cewar, Gwamnati ta ɗauki Malamai da yawa, fiye da wanda ta kora daga aiki a shekaru biyar, yana mai ƙara dacewa an ɗauki ƙwararrun Malaman Sakandire guda dubu 7,700, kuma zamu turo su, da zaran mun cire Bara Gurbi daga cikin su.
“Mun kori Malamai dubu 22,000 mun ɗauki mutane dubu 25,000. Munyi masu Jarabawa,wasu sun ƙara faɗawa sun kuma faɗi. Zamu kore su, mu dauki wasu. Mu a shirye muke mu inganta ƙwazon Malamai, domin malami shine ilmi, ba aji ba.
“Duk muna tunanin cewa ɓata garin nan, duk suje Makarantun Firamare. To yanzu dole ne zamu jijjiga Malaman Sakandire suma. Mun ɗauki Malamai dubu 7,700. Mun ɗauki matsaya cewa zamu tura ɗiyan mu a Makarantun Gwamnati.
“Na kai yaro na Makarantun Gwamnati, domin mu nunawa Al’umma cewa mun aminta da tsarin ilmin Makarantun Gwamnati, amma dole in cire shi, sabudda ƙoƙarin sace shi. Kuma bana tunanin zasu yi nasara, amma zasu sanya yaran mutane a cikin hatsari.
“Na cire shi ne. Yanzu yana karɓar ilmi a gida har sai munga yanda yanayin ya bada,” inji Gwamnan.
No comments