Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

JARUMA TABI SAHUN SADIYA HARUNA GIDAN YARI

JARUMA TABI SAHUN SADIYA HARUNA GID AN YARI Wata Babbar Kotu a Birnin Tarayya Abuja ta bada izinin sake kama Shahararriyar me siyar da Magan...


JARUMA TABI SAHUN SADIYA HARUNA GIDAN YARI

Wata Babbar Kotu a Birnin Tarayya Abuja ta bada izinin sake kama Shahararriyar me siyar da Maganin Matan nan wato Hauwa Ibrahim ( Jaruma Empire ) kotun tace,, tana bawa Hukumar 'Yan sanda dasu sake tsareta har zuwa 25th ga sabon Wata me zuwa domin ci gaba da sauraron Shari'ar, idan baku manta ba, a kwanakin Baya ne kotun ta aikewa da ita Jarumar Sammace, bayan ta bayyanan a kotun tsakanin shari'arta da Wani fittacen attajiri a Kasar nan, an bada belin Jarumar tun a wancen karon, sede yanzu kotun ta sake bada umarnin gurfa nar da Ita Jaruma a gaban Kotu, a wannan lokacin de, ita Jaruma Empire Zatayi Zaman Gidan yari ne har na kusan kwanaki 21, kuma shine karo na farko da ita Jaruma Empire ta Shiga Hannun Hukumar babu batun beli ko Rangwame, lauyan nata ya nemi a sake basu beli amma kotun bata amince da wannan korafin ba, Hakan Yasa dole Jaruma Empire Zatayi Zaman Gidan kaso a karo na farko babu batun beli daga wajen Alqali, kowa de yasan wacece Jaruma Empire, domin tayi shuhura a fannin saida maganin Mata.







No comments