Rahama Sadau ta Sadaukar da Duk kudin da ta tara a Cinema game da film ta na " Nadeeya" Rahama Sadau ta Sadaukar da Duk kudin da...
Rahama Sadau ta Sadaukar da Duk kudin da ta tara a Cinema game da film ta na " Nadeeya"
Rahama Sadau ta Sadaukar da Duk kudin da ta tara a Cinema game da film ta na " Nadeeya " wanda akalla ana tunanin ta Hada kudi kimanin Naira 3.5m Sannan Jarumar ta Sadaukar da kudin zuwa ga Gidan Marayu, kamar yadda Gidan Jarida na " HAUSA NEWS " suka rawaito, Jaruma itace daya tilo a Masana'antar fina Finan Hausa data fara irin wannan Sadaukarwar, Jama'a da dama sun yaba mata, kuma Wata kila ana tunanin ta fara biyo hanyar shiriya, bayan kalubale data taba samu a Baya a cikin Masana'antar ta Kannywood, wannan abune daya kamata a yaba mata, kuma tayi namijin kokari Matuqa, Al'umma da abokanan sana'arta sun yaba mata Matuqa, haka wasu Daga cikin Malamai a Jihar Kano sun yaba mata, duba da Irin kalubale da tasha a Baya na abin kunya daya faru da ita, Jarumar tace, tayi Hakan domin itama ta bada nata gudunmuwar a cikin Al'umma, bisa irin halin da Kasar nan ta tsinci kanta, Tabbas ya kamata a yabawa wannan Jaruma da irin namijin kokarin da tayi, kuma ta taimaki Marayu a lokacinda suke bukatar Taimakon Al'umma.
LABARAN DALLA DALLA