Shahararrun Jaruman Kannywood Guda 7 Da Suka Yi Fama Dla Matsananciyar Rashin Lafiya Kafin Rasuwarsu Da Sanadiyyar Rasuwarsu 1. Kasimu Ye...
Shahararrun Jaruman Kannywood Guda 7 Da Suka Yi Fama Dla Matsananciyar Rashin Lafiya Kafin Rasuwarsu Da Sanadiyyar Rasuwarsu
1. Kasimu Yero fitaccen É—an wasa ne wanda yana É—aya daga cikin jaruman da suka fara haskawa a gidajen kallo. Kasimu Yero ya fara fitowa a shekara ta 1980 kuma yana daya daga cikin fitattun jaruman shirin "NTA". Ya rasu ne a watan Satumba a gidansa da ke jihar Kaduna.
Kasimu yero ya rasu yana da shekaru 70 a duniya bayan ya yi fama da rashin lafiya kamar yadda dansa Mansur Kasimu Yero ya shaida wa BBC Hausa.
An yi jana’izar marigayin a Magajin Gari da ke Zariya a Jihar Kaduna kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, Allah Ya yi masa rahama.
2. Ubale ibrahim wanda aka fi sani da Wanke Wanke ya dade a masana'antar amma bai shahara kamar sauran jaruman maza ba.
Yawancin fina-finan nasa, kamfanin 2effects empire ne, mallakin wasu jarumai biyu Sani Danja da Yakubu Muhammad.
Ubale ya rasu ne a watan Mayun 2020 kafin rasuwarsa yana fama da cutar hawan jini da ciwon zuciya. An yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
3. Ladidi Muhammad wacce aka fi sani da Ladi mutu ka raba fitacciyar jarumar Kannywood, ta dade a masana'antar ta kan fito a matsayin mai rawa kafin ta fito a fina-finai.
Ladi ta rasu ne a shekarar 2020 bayan doguwar jinya. Mutane da dama sun ce ta mutu ne sakamakon ciwon daji amma jarumar ta fito ta musanta hakan kafin rasuwarta.
4. Fadila Muhammad wacce aka haifa kuma ta tashi a Jihar Kaduna, fitacciyar jaruma ce wadda ta fito a manyan fina-finai tare da fitattun jarumai irin su Ali nuhu da Adam Zango.
Fadila ta fito a fina-finai da dama amma yawancin mutane sun san ta a hubbi na fim din, amma daga baya jarumar ta bace daga masana'antar ba tare da sanin wasu dalilai ba.
Allah ya yi wa Fadila Muhammad Muhammad rasuwa a watan Agusta 2020. Jaruman Kannywood da dama sun bayyana alhininsu kan rashin ta. Fadila ta rasu ne sakamakon bugun zuciya.
No comments