Shin Kunsan Matan Kannywood Da Adam A Zango Yayi Soyayya Da Su, da baku sani ba SOYAYYAR ADAM ZANGO DA MATAN KANNYWOOD Ko kunsan cewa Adam ...
Shin Kunsan Matan Kannywood Da Adam A Zango Yayi Soyayya Da Su, da baku sani ba
SOYAYYAR ADAM ZANGO DA MATAN KANNYWOOD
Ko kunsan cewa Adam A Zango yayi soyayya da mafi yawancin shahararrun matan kannywood?
Adam A Zango dai jarumi ne a masana'antar kannywood da kurar sa tayi kuka ta fuskar yaudara da son mata inda duk wacce ya gani a masana'antar kannywood baya iya kauda idon sa face sai ya kai mata tayin soyayyar sa. Inda a sakamakon haka ne jaumin yayi soyayya da fiye da rabin jauman kannywood. Kamar haka:
1. NAFISA ABDULLAHI
Nafisa Abdullahi dai tana daya daga cikin shahararrun jarumai mata da tauraron sun yake haskawa inda a baya bayan nan ne ma ta ja ragamar wani fim mai dogon zango mai suna Labarina shirin da yayi tasiri a zukatan masu kallo.
Adam A Zango yayi soyayya da Nafisa Abdullahi inda har ya tabbatar mata da cewa zai aure ta amma a karshe ya yi kunnen uwar shegu da lamarinta.
2. FATI WASHA
Fatima Abdullahi wadda aka fi sani sa fati washa ta kasance daya daga cikin matan kannywood da Adam Zango ya yi soyayya da ita. Fati washa dai kyakykyawa ce son kowa kuma shahararriya a masana'antar kannywood wadda tayi fice ta fuskoki da dama wadda itama Adam A Zango bai aure ta ba.
3. AISHA ALIYU TSAMIYA
Aisha Tsamiya na daya daga cikin matan kannywood da dadin bakin Adam A Zango ya ritsa da ita domin kuwa sunyi ta fitowa a cikin fina finai tare inda hakan ya sa jama'a suka kara gaskata maganar auren Adam Zango da ita, amma itama Adam Zango yayi watsi da shaannin ta.
4. SADIYA GYALE
Sadiya Gyale dai tana daya daga cikin matan kannywood da suka raini masana'antar ta kannywood domin kuwa har yanzu da bazar su ake rawa. Sadiya Gyale ta taka rawar gani sosai a masana'antar fina finan Hausa.
Adam A Zango bai tsagaita ba saida ya mika kokon sa na barar soyayyar jaruma Sadiya Gyale inda ta amince masa amma daga baya ya rabu da ita.
5. UMMI RAHAB
Matashiya kuma kyakykyawar yarinya son kowa tana daya daga cikin matan kannywood da fuskokin su suke haskawa. Ita ma Adam Zango ya yi soyayya da ita inda hakan ya jawo cece kuce a masana'antar kannywood yayin duniya ta dauka gaba daya.
Sai dai a wannan karon jarumi Adam Zango ya sha wuya sosai domin kuwa bai taba soyayya mai wahalar ta saboda ta yawo masa surutai masu yawa.
6. RAHAMA SADAU
Ita ma Rahama Saudau ba a barta a baya ba domin kuwa ta dandana kalaman soyayya daga baki Adam Zango wanda hakan yasa ita ma ta fada soyayya ka'in da na'in da Jarumin amma tafiyar bata dade ba aka ki dadaitawa a nan ne suka rabu kowa ya kama hanayar sa.
6. HALIMA ATETE
Ta kasance 'yar kabailar Kanuri kuma kyakykyawa jaruma da ta sami haskawa a masana'antar kannywood dake arewacin Nijeriya. Itama jarumi Adam Zango ya kai mata farmaki da makami mai linzami inda ya sace mata zuciya kuma inda ta antaya cikin kogin kaunar sa amma itama a karshe ta gane cewa hanyar ba mai bullewa bace, inda ta fece.
7. ZAINAB INDOMIE
Ita har zama ma tayi a karkashin kulawar sa. Tun lokacin da tayi rashin lafiya Zainab Indomie ta kasance a karkashin kulawar jarumi Adam Zango har ta sami sauki.
Ita ma dai jarumar tana daya daga cikin matan kannywood da suka yi tashe kwarai da gaske in suka fito a fina finai da dama tare da jarumi Adam Zango. Daya daga cikin fina finan shine Dowo Dawo tare da jarumi Ali Nuhu wanda ake yiwa kirari sa Sarki.
A wannan fim mai suna Dawo Dawo jaruma Zainab Indomi ta baje kolinta sosai inda ta yi ta gasawa kanwarta aya a hannu wato maryam Booth da Adam Zango.
Ita ma dai soyayyar tasu shiru kake ji...
No comments