WANNAN ABIN TSORO NE GA MAKOMAR YARAN MUSULMI DAGA Datti Assalafiy Ban taba tsammanin lalaacewar 'yan Hausa film da yaada barnansu da i...
WANNAN ABIN TSORO NE GA MAKOMAR YARAN MUSULMI
DAGA Datti Assalafiy
Ban taba tsammanin lalaacewar 'yan Hausa film da yaada barnansu da iskancii har ya kawo wannan matakin ba.
Wannan shirin film ne na Hausa wanda ake sakawa a shafin wani shahararren mawakin Hausa Film Nazifi Asnanic.
Babu abinda yake cikin shirin film din mai suna BINTALO sai zallar iskanci da lalata, wannan shine tarbiyyan da sukace suna koyarwa a Arewa.
Muna kira ga Maigirma Gwamnan jihar Kano
Muna kira ga Maigirma Sarkin Kano
Muna kira ga hukumar tace fina-finai na jihar Kano ku hadu ku dauki mataki akan wanda ya shirya wannan film.
Muna rokon Allah Ya kare Musulunci daga abinda 'yan Hausa film suke yadawa na ruguje tarbiyya da addini.
No comments