ALAQA Episode 14 Subtitle In English *SHARHI AKAN FILM DIN ALAQA* ALAQA dai wani sabon fim ne mai dogon zango da ake nunawa duk ranar Juma...
ALAQA Episode 14 Subtitle In English
*SHARHI AKAN FILM DIN ALAQA*
ALAQA dai wani sabon fim ne mai dogon zango da ake nunawa duk ranar Juma'a da karfe takwas na dare (08:00pm) a tashar *Ali Nuhu TV* wato tashar jarumi Ali Nuhu (Sarki).
Shirin fim din *ALAQA* yazo da wani sabon salo wanda zamu iya cewa ba duk kai ba domin kuwa shirin yana nuna zallar irin al'amuran da suke faruwa a wannan rayuwa tamu ta yau da kullum, musamman ma a wannan nahiya.
Wannan fim *ALAQA* jan hakali ne da kuma nuni akan abubuwan dake faruwa a zahiri ta yadda mutum zai dauki darussa daban daban domin yasan ta ina zai bullowa rayuwa da irin mutanen da ya kamata yayi mu'amala dasu domin tsira da mutunci.
Sannan shi wannan fim yana fayyace asalin abubuwan dake faruwa a siyasa ta yadda wasu suke amfani da mutanen da basu san ciwon kansu ba a, kuma marasa tsoron Allãh a hada baki dasu su shiga jikin mutane masu mutunci da kima domin su bata musu suna kawai saboda abin duniya da bai taka kara ya karya ba.
Fim din *ALAQA* ya tara fitattu da kuma matasan yan fim wato jarumai masu tasowa kamar haka:
Ali Nuhu
Tahir M. Fagge
Lawal Ahmad
Baballe Hayatu
Aminu S. Bono
Ramadan Booth
Shamsiddin Dan'iya
Hafsat Idris
Momi Gombe
Malam Haruna
Auwal Adam West
Fatima (Teema Makamashi)
Bilkisu Abubakar
Ladin Cima da sauran su. Sai kun kalla zaku ga yadda kowa ya baje irin bajintar da Allah Ya masa.
*YAKUBU ADAM ABUBAKAR (YACKSON)*